An tsinci wani Jariri Sabon haihuwa kulle cikin leda a magudanan Ruwa A Minna


A safiyar ranar Talata ne dai wani ɗan Jari bola ya tsinci wata jaka a cikin bega inda ruwa ke wuce wa inda yayi tunanin cewa kakarsa ta yanke saka. Sai dai bude ledar keda wuya sai ga jariri sabon haihuwa ƙulle a cikin leda ko mahaifa ba'a yanke masa ba.


Lamarin ya faru ne a Unguwar Paida dake garin na Minna inda al'umma suka nuna rashin jindadin su game da ganin irin wannan irin rashin imanin mafi muni.


Wani da ya nemi da a sakaye sunan sa yace ko domin irin wannan munanan ayyukan da al'umma suke aikatawa dole a ringa ganin musibu kala-kala, inda ya ƙara da cewa dole mu canza hali mu koma nagari domin ganin dai-dai a rayuwa.


Yarda jariri dai ba sabon abu bane, domin ko a watan da ya gabata ansamu makamancin faruwar hakan a garin na Minna. Sai dai jama'a na bayyana cewa akwai sakacin hukuma na rashin ɗaukar mataki da yin hukunci akan wanda aka samu da aikata irin wannan laifin.


Daga Hafsat Adam 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post