ALLAHU AKBAR: Ya Rasu Bayan Awa Guda Da Canja Hotonsa A Shafin Sa Na Facebook


Haƙiƙa mutuwar mutum cikin koshin lafiya akwai tayar da hankali. Mutuwar da ba'a tsammanin ta ga mutum akwai matuƙar tada hankali.


Sai dai ita mutuwa kowa akwai sanadin da take riskarsa. Wani sai ya yi doguwar jiyya wani kuwa jinyar gajeren lokaci. Wani kuwa kuwa babu wata jiyya kodai hatsari ko kuma makamancin haka sai ajali.


Haka shima wannan saurayin Allah ya kawo masa nasa sanadin ƙaddara mutuwarsa. Malam Sirajo an ruwaito cewa ƙasa da awa ɗaya kafin rasuwarsa yana cikin ƙoshin lafiya tare da gudanar da ayyukan sa na yau da kullum.


Ko a shafin sa na facebook anga ya canja hoton sa dake kan profile ya saka wani daban. To ashe shine hawan sa na karshe ba zai sake hawa ba. Haƙiƙa mutuwar ta girgiza mutane sosai.


Wannan yana ƙara nuna mana cewa ita mutuwa a koda yaushe tana iya riskar mutum koda lafiya ko babu ita, ko mutum ya shirya ko bai shirya ba, kuma ko mutum yana so ko baya so.


Shi dai Malami Sirajo na Gidan Guruza dake Kofar Dindi ya rasu a sanadiyar haɗarin mota a bakin gidan Alu Kyalla.


Allah ya sa ya huta, Allah ya kai haske kabarinsa. Mu kuma Allah yasa muyi kyakkyawar ƙarshe Amin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post