Labari Mai Cike Da Sosa Zuciya: Rayuwata Tana Cikin Baƙin Ciki Mai TsananiNa auri matata shekaru 25 da suka wuce, ta zo da yara maza biyu daga gidan auren da ta yi a baya. Ina matukar son su kuma na ɗauki yaran tunda ni bani da isasshiyar lafiya ballantana in haifi nawa yaran.


Mun zauna lafiya a gidajen haya.  Ina aiki a lokacin kuma na tabbatar da cewa na kai ƴaƴan da na yi reno zuwa mafi kyawun makarantu, uban yaran bai taɓa zuwa neman su ko ma tallafa musu ba.


Yaran sun yi haske suna kuma jindaɗi sosai, a fannin karatu kuma yayin da nake rubuta wannan, ɗaya daga cikin yaran likita ne wanda ya sami gurbin karatu don kammala karatunsa a Amurka wanda a yanzu haka ya fara aiki.


Yaron na biyu kuma matuƙin jirgi ne wanda na yi amfani da duk kuɗin da na samu wajen biyan kuɗin kwas ɗin sa a Afirka ta Kudu, shi ma yana aiki yanzu haka da nake wannan rubutun.


Abin farin cikina shi ne samarin nawa sun yi nasara sun sayi manyan gidaje, matsalata ita ce matar tawa wato mahaifiyar yaran biyu sun sake haɗuwa da mahaifinsu kuma yanzu suna zaune lafiya tare a matsayin iyali.


Da alama sun watsar da ni a nan, ba ma iya biyan haya na, na yi ritaya tuntuni, ina ƙaura daga wani wuri zuwa wani wurin domin kawai in samu inda zan kwana, yanzu ko kiran wayata suka gani basa ɗauka wannan shi ne sakayyar da suka nunamin. Sun banzatar dani sun manta da dukkan ɗawainiyar danai musu a baya. Don Allah me zan yi yanzu ?


Daga Aliyu Adamu Tsiga

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post