Ayyukan da suka fi falala A kwanaki goma na farkon Watan Hajji


A cikin wannan kwanaki 10 na Zul Hajji wanda bayyana cewa kwananki ne masu girma da daraja da babu kamar su. Don haka ne ake kwadaitar da al'umma musulmi irin abubuwan da ya kamata su shagaltu da yin su a cikin wadannan kwanaki masu girma. Ga wasu daga cikin abubuwan da ake bukatar duk musulmi yai kamar haka.


1. Sallar Nafila Ta Dare.


Allah Subhanahu wa taala Yayi rantsuwa da wasu lokutta domin nuna mahimmancinsu. Allah Yace:  {وَالْفَجْرِ (1) وَلَيَالٍ عَشْرٍ} [الفجر: 1، 2]  Maana: (1. Inã rantsuwa da alfijiri.  2. Da darũruwa gõma.) Saboda haka Sallar nafilar dare musamman a lokacin sulusin dare na karshe tana da falala sosai.


2. Aikin Hajji da Umra.


3. Layya ranar Goma ga watan.


An ruwaito hadisi daga Aisha – radiyallahu ‘anha tana cewa: 


 (عن عائشة : أن رسول الله صلى الله عليه و سلم قال ما عمل آدمي من عمل يوم النحر أحب إلى الله من إهراق الدم إنها لتأتي يوم القيامة بقرونها وأشعارها وأظلافها وأن الدم ليقع من الله بمكان قبل أن يقع من الأرض فيطيبوا بها نفسا). رواه الترمذي والحاكم.


(Manzon Allah – Tsira da amincin Allah su tabbata agareshi – yace: Dan Adam bai aikata wani aiki ba ranar layya wanda yafi soyuwa zuwa ga Allah kamar zubar da jinin layya domin ko lalle zata zo ranar tashin kiyama da kohoninta  da gashinta da kofatunta, kuma jininta yakan fada a wurin Allah ga wani wuri kafin ya zuba a kan kasa, saboda haka ku farantar da ita layyar wani rai.)


4. Azumin ranar Arafat ga mauzana gida.

Muslim ya ruwaito hadisi cewa an tambayi Manzon Allah – Tsira da amincin Allah su tabbata agareshi –:

(Game da azumi ranar Arafat sai yace: yana kankare zunuban shekarar baya da wanda ta rage)


قَالَ وَسُئِلَ عَنْ صَوْمِ يَوْمِ عَرَفَةَ فَقَالَ « يُكَفِّرُ السَّنَةَ الْمَاضِيَةَ وَالْبَاقِيَةَ » مسلم


5. Sauran ayyukun alheri na kamar karanta alqurani, tasbihi, takbiri, azumin nafila, sadaqa, da sauransu.

An ruwaito hadisi daga Aisha – radiyallahu ‘anha tana cewa: 


عنْ عَائِشَةَ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صلى الله عليه وسلم قَالَ : سَدِّدُوا وَقَارِبُوا وَاعْلَمُوا أَنْ لَنْ يُدْخِلَ أَحَدَكُمْ عَمَلُهُ الْجَنَّةَ ، وَأَنَّ أَحَبَّ الأَعْمَالِ أَدْوَمُهَا إِلَى اللهِ وَإِنْ قَلّ. رواه البخاري


Kuyi saiti (wurin dacewa da ayyuka) ku yi kusanci (wurin samun daidai a ayyukka) kuma ku sani cewa ba wanda aikinsa zai shigar dashi aljannah, kuma mafi soyayyen ayyuka a wurin Allah sune wadanda aka dawwama akansu ko da kadan ne basu da yawa.

Allah Ya bamu dacewa kuma Ya karbi Ayyukan mu na ajizai masu gazawa. Amin

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post