Ruwan Sama Mai Karfin Gaske Ya Jawo Ambaliya Wanda Yai Sanadin Rushewar Gidaje Fiye Da 2,000 A Kano


A sakamakon wani mamakon ruwa da mai ƙarfin gaske tare da guguwar iska ya jawo lalacewar dimbin gidaje da yawan su ya haura dubu 2,000 a jihar Kano, a cewar wani rahoto da Jaridar DAILY TRUST ta fitar.


Aƙalla mutum uku ne suka rasa rayukansu yayin da gidaje 2,250 suka hallaka sanadiyyar wata Ambaliya da mamakon ruwan sama a ƙananan hukumomi biyar na jihar Kano. Shugaban hukumar kai ɗaukin gaggawa ta jihar Kano, SEMA, Dakta Sale Jili, shi ne ya bayyana haka yayin zantawa da jaridar DAILY TRUST.


A cewarsa, ƙananan hukumomin da lamarin Ambaliyar ya shafa sune: Rano, Kibiya, Doguwa, Danbatta da kuma Kiru. Bayan aukuwar wannan lamarin, Dakta Sale Jili, ya shawarci baki ɗaya mutanen da ke zaune a dukkan sassan jihar Kano da su samar wa ruwa hanya ta hanyar gyara hanyoyin Lambatu da ke gaban gidajen su. 


A jawabinsa ya ce: "Hukumar kula da hasashen yanayi (NiMeT) ta bayyana hasashenta na ruwan sama a daminar bana 2022, inda ta yi hasashen saukar ruwan sama mai tsanani a jihar Kano." "Mun ɗauki matakan kai agajin gaggawa ta hanyar ziyartar dukkan yankunan da abun ya shafa don jajantawa mutanen da lamarin ya taba da kuma raba musu kayan rage radaɗi a madadin gwamnatin jiha." 


Wane mataki zasu ɗauka nan gaba? Bugu da ƙari, Dakta Saleh ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen kokarin da take na kare rayuka da dukiyoyin al'ummarta. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post