Harin da ƴan bindiga suka kai coci a kaduna yai sanadin mutuwar mutane da dama


A Najeriya ƴan bindiga sun afka wa masu ibada a cocin Maranatha da cocin Saint Moses Catholic Church a kauyen rubu da ke a karamar hukumar Kajuru ta jihar kaduna inda suka kashe mutane 3.


Jaridar Daily trust da ake wallafawa a kasar ta ruwaito cewa mutane 2 sun samu rauni a yayin kai haren-haren da maharan suka kai bisa Babura a ranar Lahadi, jim kaɗan bayan da aka tashi daga sujjada.


RFI Hausa ta rawaito cewa maharan sun yi awon gaba da mutanen da ba a tantance adadinsu ba a kauyuka biyu na garin Rubu da suka kai hare-haren.


A yayin da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel aruwan, yace maharan sun fara ta’asa ne daga Unguwar Fada, kana suka nosa Unguwar Turawa, kafin su Karkare a unguwar Makama, sai kuma kauyen Rubu.


Ko a makon da ya gabata a jihar Edo an samu faruwar irin wannan al'amari inda wasu ƴan bindiga suka shiga cikin coci suka buɗe wuta wanda yai sanadin mutuwar mutane da dama

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post