Yadda dakarun soji suka hallaka mayaƙan ISWAP da ba'a san adadin su ba a tafkin ChadiDakarun Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasa da Kasa (MNJTF) na Jamhuriyar Nijar sun samu nasarar kashe gommai na mayaƙan ISWAP a wani hari da suka kai kan maɓoƴar su da ke Arewa maso Gabashin Tafkin Chadi.


Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa sojojin sun kai farmaki kan maɓoƴar ƴan ta’addan ne a cikin ƙuryar ƙauyen Ndaurori, wani gari mai iyaka da Najeriya da Jamhuriyar Nijar.


Wata majiyar leken asiri ce ta shaida wa Zagazola Makama, wani masani kan yaƙi da tayar da ƙayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi. A cewarta, an kashe mayaƙan da ba a tabbatar da adadinsu ba a yayin da wasu suka gudu da raunukan harsashi a jikin su.


Majiyar ta kara da cewa, harin da dakarun suka kai ya tilastawa ƴan ta’addan da suka tsere neman wurin ɓuya a garin Bulabulin mai tazarar kilomita 28 daga Damasak.


Hakazalika, majiyar ta ce mayaƙan na amfani da maɓoƴar da suka fake domin kula da ƴan uwansu da suka jikkata.


Rundunar sojin ta (MNJTF) a waɗannan makonnin suna taka rawar gani wajen murƙushe ƴan tada ƙayar baya a yankin na tafkin Chadi.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post