Yajin Aikin ASSU: Ɗalibai Sun yi barazanar rufe filayen jiragen sama na ƙasar - Android Pols


A ranar Litinin ne Ƙungiyar Ɗalibai ta Ƙasa, NANS, suka yi barazanar rufe manyan filayen jiragen saman ƙasar idan har aka ci gaba da jayayya tsakanin Ƙungiyar Malaman Jami'o'i, ASUU da gwamnatin tarayya.


Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, Adegboye Olatunji ne ya bayyana haka a Abuja a ranar Litinin, a wata zanga-zanga da su ka yi a sakateriyar jam’iyyar APC, ta nuna goyon bayan Gwamna Dapo Abiodun na Ogun domin ya tsaya takara karo na biyu.


Olatunji ya ce lokaci ya yi da ɓangarorin biyu za su haɗu domin warware matsalolin da suka haddasa yajin aikin saboda ɗalibai ne ke illatuwa da hakan. “Muna shirin mu toshe ma'aikatun gwamnati da ke samar mata kuɗi idan har ba a warware matsalar ASUU ba.


“Mun yi zanga-zanga a kan wannan batu ta hanyar mamaye manyan tituna a yankin Kudu-maso-Yamma amma muna ganin idan muka rufe filayen jiragen sama, gwamnati za ta yi wani abu game da yajin aikin,” inji shi.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post