Mayaƙan Boko Haram fiye da dubu 50 ne suka ajiye makaman su



Shelkwatar tsaron Najeriya ta ce ya zuwa ranar 16 ga watan Mayun 2022 mayaƙan Boko Haram 53,262 ne suka miƙa wuya ga hukumomin tsaron ƙasar.


Ta ce mambobin kungiyar 1,627 sun mika wuya tare da iyalansu, ciki har da maza 331 da mata 441 da yara 855 sun mika wuya ga sojoji a yankuna daban-daban tsakanin 1 ga watan Mayu da kuma 14 ga watan.


Daraktan Shelkwatar ta bangaren watsa labarai, Manjo Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan a birnin Abuja. Inda yace dakarun Najeriya na rundunar haɗin kai sun kashe ƴan ta’adda 43, tare da kama 20 da kuma ceto mutum 63 cikin waɗanda aka kama a faɗin arewa maso gabahsin ƙasar cikin mako uku.


Ya ce sun kashe kwamandan Boko Haram Abubakar Sarki a dajin Sambisa a Yuwe da ke cikin ƙaramar hukumar Konduga a jihar Borno.


Kawo yanzu dai ana ta samun mayaƙan da suka addabi yankin arewa maso gabas suna ajiye makaman su, wanda hakan yake nuna alama ta samun nasara da sojoji suke yi wajen kawo ƙarshen ayyukan ta'adanci a yankunan.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post