Ƴan ta'adan IPOB sun sare kan wani ɗan majalisa a jihar Anambra - Android Pols


Wasu ƴan bindiga da a ke kyautata zaton ƴan haramtacciyar ƙungiyar nan ce mai neman warewa daga Najeriya ta IPOB sun fille kan wani ɗan majalisar dokokin Jihar Anambra, Dakta Okechukwu Okoye, bayan sun yi garkuwa da shi.


A ranar Lahadin da ta gabata ne ƴan bindigan su ka sace ɗan majalisar da ake kira “Okey Di Okay” da ke wakiltar Aguata ta arewa, mazaɓar gwamnan Anambra, Farfesa Chukwuma Chukwuma Soludo.


Bayanai sun ce an tsinci kan ne da aka fille a gefen hanya tare da wata wasiƙa a yankin Amichi a Anambra. Rundunar ƴan sandan Anambra cikin wata sanarwa game da al’amarin ta ce a yayin gudanar da bincike wasu mutane sun tsinci gawar mutum, wanda aka tantance gawar ɗan majalisar ce Hon Okechukwu Okoye.


Ƴan kwanakin nan dai hare-haren ƴan tada ƙayar baya na IPOB sai Ƙaruwa yake yi, wanda hakan ke jawo asarar rayuka a yankunan. Dama dai ko a satin da ya gabata sai da gwamnan jihar Anambra ya ziyarci shugaban ƴan aware na IPOB wanda wasu ke ganin hakan ba daidai bane.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post