Shehin Malami Ibrahim Khalil Ya Zama Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam'iyar ADC


Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Dr Malam Ibrahim Khalil, ya zama ɗan takarar Gwamnan Jihar Kano a jam’iyyar ADC.


Jaridar Aminiya ta rawaito cewa, Malamin ya sayi fom ɗin takarar ne kan Naira miliyan 10 sannan zai zama ɗan takarar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa kasancewar shi kaɗai ne ya sayi fom ɗin kujerar takarar gwamnan a jam'iyar ta ADC.


A cewar Shugaban jam’iyyar ta ADC a Jihar Kano, Musa Shu’aibu Ungogo, shugabannin jam’iyyar ne da kan su suka yanke shawarar zuwa har Jihar Kano don kawo masa fom ɗin saboda muhimmancinsa aJihar.


Ya ce, “Dukkan sauran masu neman takara sukan je hedkwatar jam’iyyar ne a Abuja don sayen fom, amma shi Sheikh Khalil bayan ya biya kuɗin, sai suka ce ya dawo za su kawo masa har gida.


“Hakan ne ya sa Shugaban jam’iyyar na ƙasa da Sakatarensa da kuma Mataimakin Shugaba na Shiyyar Arewa maso Yamma suka zo har Kano don gabatar masa da fom ɗin, a cewar rahoton Aminiya.


“Shugaban ya kuma yi amfani da bikin wajen rantsar da Shugabannin shiyyar Arewa maso Yamma na jam’iyyar, karkashin Farfesa Kabiru Dandago. Ya ce ya zuwa yanzu, Shehin Malamin ne kawai ya sayi fom ɗin takarar Gwamnan a Jihar.


Shugaban jam’iyyar ya kuma yi kira ga mutanen Jihar da su yi watsi da jam’iyun APC da PDP saboda ya ce su ne suka kashe Najeriya, inda ya ce ADC ta sha bamban da sauran jam'iyun.


Idan za'a iya tunawa, a watannin baya ne dai Sheikh Ibrahim Khalil ya sanar da ficewarsa daga APC sannan daga bisani ya koma ADC. A zabukan baya, ya taɓa neman takarar kujerar a jam’iyyar APC, amma bai yi nasara a zaɓen fitar da gwani ba.


Jama'a dai suna ta bayyana ra'ayin su akan fitowar takarar gwamna da Malam Ibrahim Khalil yai, wanda wasu ke ganin cewa irin su ne Malamai ya kamata su ringa fitowa suna shugabantar al'umma, domin za su kawo gyara da cigaba tare da yin adalci.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post