Shugaba Muhammadu Buhari ya saka hannu kan dokar Kara Kudin kiran waya


Shugaban Najeriya Muhammadu ya rattaba hannu kan sabuwar dokar ƙarin kuɗaɗen haraji ga masu kiran waya a ƙasar baki ɗaya.


Jaridar RFI Hausa ta rawaito cewa, hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar, inda ta ce za’a yi karin kwabo guda kan kowanne kiran waya da ɗan Najeriya zai yi, ƙari kan abinda aka saba biya.


Ta cikin sanarwar fadar shugaban Najeriyar ta ce za’a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen taimakawa gajiyayyu da kuma zuba su don tsamo tattalin arzikin ƙasar daga mawuyacin halin da yake ciki.


Ko da sanarwar ta ci gaba da ƙarin bayani ta ce za’a fi karkata kuɗaɗen ne ga ɓangaren lafiyar gajiyayyu da masu buƙata ta musamman don inganta lafiyar su.


Tuni dai ƴan Najeriya suka fara yiwa sabuwar dokar bore, a ganin su halin da tattalin arziƙin Najeriya ke ciki kamata ya yi a ragewa ɗan Najeriya harajin da yake biya ba wai ƙara masa ba.


Tun a shekaraun da suka gabata kamfanin kiran waya da suke aiki a Najeriya sun yi barazanar ƙara kuɗin kiran waya sakamakon ƙarin kuɗin haraji da gwamnatin tarayya tai musu. Sai dai mahukunta basu yarda sun yi ƙarin kuɗin kiran ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post