Matashiyar Da Aka Bata Kuɗi Sama Da Miliyan Ɗaya Domin Ta Kwanta Da Kare Ta Mutu


A ƴan kwanakin nan duk masu bibiyar labarai za su ci karo da labarin wata budurwa mai suna Mirabel wanda labarinta yake ta watsuwa cewar an bata kuɗi million ɗaya da dubu dari bakwai domin ta sadu da kare a yankin Lekki na jihar Lagos.


Kamar yadda jaridar Daily Independent ta ruwaito, wani ganau ya bayyana cewa tun a ranar Lahadin makon da ya gabata ne matar ta fara karbar magani a wani asibiti bayan da ta fara jin alamun rashin lafiya a jikin ta.


To ta mutu ranar litinin saboda wata cuta da ta ɗauka sakamakon saduwar da tayi da wannan karen ance sunan cutar "Canine Brucellosis" wanda a jikin kare ne ake samun irin wannan cutukan. Mirabel ta mutu a ranar Litinin a wani asibiti da ba'a bayyana sunansa ba a cikin Lagos.


Mutuwar wannan yarinyar zai zama darasi ga irin mutanen da ake biya kuɗi domin a saka musu wani abu ace idan sun aikata to wannan kuɗin ya zama mallakin su. Wanda kuma a ƙarshe yakan jawo halaka ga mutum.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post