Yadda Sojoji Suka Yi Nasarar Kashe, Ɗan Ta'addan Da Ya Addabi Yankin Ɗansadau A Jahar Zamfara


A ranar Talata ne wani rahoto da ya fito daga jihar Zamfara ya tabbatar da cewa jami'an soji sun yi nasarar hallaka ƙasurgumin ɗan ta'ada da ya daɗe yana addabar yankin Ɗansadau ta jihar Zamfara.


Shi dai dai ɗan ta'adan da ake yiwa kirari da Damina ya shafe tsawon lokaci yana kashe mutane tare da yin garkuwa dasu domin karɓar kuɗin fansa. Kuma jami'an tsaro sun sha yi masa tarko amma basu samu nasara ba.


Sai dai a ranar Talata a yayin wani artabu da ya gudana tsakanin ƴan bindiga da jami'an tsaro wanda hakan yai sanadin mutuwar ƴan bindiga da dama ciki har da Damina.


Al'umma dai a jihar na ta nuna farin cikinsu game da mutuwar wannan ƙasurgumin ɗan fashin da ya buwayi kowa da kowa jihar.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post