Ƴan Ta'ada Sun Kashe Sojoji 7 Tare Da Wani Janar A Jihar TarabaAna fargabar wasu ƴan bindiga a Jihar Taraba da ke Arewacin Najeriya da kashe kwamandan sojin Bataliya ta 93 dake Takum mai riƙe da muƙamin Birgediya Janar tare da wasu sojojin sa 7.


Gidan Jaridar RFI Hausa ya wallafawa cewa mahukunta a jihar ta Taraba su tabbatar da kai harin daga bakin shugaban ƙaramar Hukumar Takum Hon Shiban Tikari, amma bai yi ƙarin haske akan yadda lamarin ya faru ba.


Tikari ya ce yanzu haka shi da wasu jami’an tsaro na jeji inda suke ƙoƙarin gano gawarwakin sauran sojojin dake tawagar Kwamandan da suka ɓace.


Jaridar ta ruwaito shaidar gani da ido na cewa an samu aukuwar lamarin ne tsakanin Takum zuwa ƙauyen Tanti akan hanyar zuwa Jalingo.


Majiyar ta ce Kwamandan na kan hanyar zuwa Jalingo ne a lokacin da ƴan bindigar suka yi wa tawagarsa kwantan ɓauna.


Ita ma dai jihar Taraba a cikin wannan watannin suna fuskantar matsalolin hare-haren ƴan bindiga wanda ke haddasa rasa rayukan al'umma tare da dukiyoyi. Wasu na zargin cewa ƴan Boko Haram ne daga yankin arewa maso gabas suke shigowa yankin jihar Taraba suna kai hare-haren.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post