BINCIKE: Wata Zaiyi Zazzaɓi Ranar Litinin A Najeriya


A ranar Litinin ne 16 ga watan Mayu 2022 za'a samu kisfewar rana a Najeriya da wasu sassan ƙasashen Afrika a cewar wani masanin ilmin taurari Farfesa Augustine Ubachukwu.


Farfesan wanda shine shugaban tawagar masu binciken ilimin sanin taurari a jami'ar Najeriya dake NSUKA a jihar Enugu ya bayyana Hakan ne a wata hira da yai da kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN). Sannan ya ƙara da cewa binciken ya nuna za'a samu kisfewa ta biyu a ranar 2 ga watan Nuwamba 2022.


Hakazalika, ya ce kowanne wata, za a samu jinjirin wata da zai zagaye duniya ta tsakaninta da rana, daga nan kuma ya zagaye duniyar ta wani ɓangaren daban ya fito a cikakkensa. Ya kuma ce idan aka samu abubuwa uku a sararin samaniya sun jeru da juna, ko shakka babu ko dai a samu kisfewar wata ko kuma ta rana.


Masana kimiyya dai sun bayyana cewa idan wata ya bi ta inuwar duniya shi ne ake samun kisfewarsa. Sun ce dama lokaci zuwa lokaci akan samu hakan ya faru, don haka canjin yanayi ne yakan kawo haka bayan tsawon lokaci.


Masana sun bayyana cewa akan samu kisfewar wata da rana a sassa daban-daban na faɗin duniya musamman a nahiyoyin Kudancin Amirka da yammacin Turai.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post