Ɗalibai A Kwalejin Shagari Sun Kashe Wata Ɗaliba Tare Da Ƙona Ta Akan Yin Ɓatanci Ga AnnabiWata ɗaliba da aka lakaɗa mata duka har ta mutu sannan kuma aka ƙone gawar ta saboda zargin cin mutunci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) a kwalejin ilimi ta Shagari dake jihar Sokoto.


Jaridar PUNCH ta rawaito cewa ɗalibai ne musulmai suka ƙone gawar ta har lahira, inda suka fito da ita daga ɗakin kwanan ta. Matashiyar dai ɗaliba ce a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke jihar Sokoto, wadda har zuwa yanzu ba'a gama tantance asalin yadda lamarin ya faru ba.


Sai dai wata majiya ta bayyana cewa matashiyar ta rasa ranta ne a hannun abokan Karatun ta bisa zargin ta da zagin Annabi Muhammad (SAW).


SaharaReporters ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis. Inda ɗalibai musulmi ne suka ƙone ta har lahira, inda suka fito da ita daga ɗakin kwanan ta.


Hakazalika idan ba'a manta ba a watan Maris ɗin 2021, wasu fusatattun matasa da shugabanni ke marawa baya a yankin Sade da ke karamar hukumar Darazo ta jihar Bauchi, suka ƙona wani mutum mai suna Talle Mai Ruwa, har lahira bisa zarginsa da zagin Annabi Muhammad (SAW).


An gano cewa an ciro Mai Ruwa daga gidansa a ranar Talata a gaban mahaifiyarsa kuma aka ƙona shi har lahira a tsakiyar al’umma. Shedun gani da ido sun raba hotunan yadda lamarin ya faru ga manema labarai wanda suka nuna matashin mai matsakaicin shekaru an ƙone shi.


Mahukunta dai suna yawan jan hankalin matasa da su daina saurin ɗaukar hukunci da hannun su idan irin hakan ya faru. Hukuma itace take da alhakin yim hukunci daidai da irin laifin da mutum ya aikata. Yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW) babban laifi ne amma ba'a bada umarnin mutane su ɗauki hukunci a hannu ba.
Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post