Haɗakar Soji Ta MNJTF Sun kashe ƴan Boko Haram Fiye Da 300 A Tafkin Chadi.


Rundunar haɗin gwiwa ta Multinational Joint Task Force, MNJTF, a ranar Asabar ta ce ta hallaka mayaƙan Boko Haram da ƴan ISWAP 300, a tafkin Chadi dake yankin Arewa-maso-Gabas.


Dakarun soji na hadak na MNJTF sun ƙunshi sojin Kamaru, Chadi, Nijar, Najeriya da Benin. Kamarudeen Adegoke, babban jami’in yaɗa labarai na rundunar soji ta MNJTF N’Djamena, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Maiduguri, ya ce an kashe ƴan ta’addar ne a arangama daban-daban.


Adegoke, wanda ya ke da muƙamin Laftanar-Kanar, ya bayyana cewa, Kwamandan rundunar, Abdul Khalifa, ya bayyana haka a lokacin wani taro da ɗaukacin kwamandojin MNJTF da aka zaɓo daga kowane ɓangare.


Ya ƙara da cewa mayaƙa sama da 52,000 da iyalansu suka miƙa wuya ga rundunar MNJTF. Ya kuma yi kira ga ƴan ta’addan, da su ƴan Boko Haram ne ko kuma ISWAP ne, da su yi fita da ga wannan ƙungiyar ta masu aikata laifuka su kuma miƙa wuya kamar yadda dubban ƴan uwansu suka yi kafin lokaci ya ƙure musu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post