Ƙaunar Adam A. Zango Kullum Ƙaruwa Takeyi A Zuciya Ta - Cewar Safiya Chalawa


Matar jarumi a Masana’antar Kannywood, Adam A. Zango, Safiya Challawa ta bayyana yadda a kullum take ƙara son shi a zuciyar ta. Safiya Challawa ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram, inda ta ce kulawar da yake nuna mata ne ya sa a kullum take ƙara son shi a zuciyar ta.


Irin kulawar da kake nuna min a kullum take ƙara min tsananin ƙaunar ka. Ba zan taɓa mantawa da ranar cikar burina ba, ranar da wanda nake so ya nuna min soyayyarsa a fili. Wato ranar aurenmu.


“Da a ce zan iya zama komai, da na zama ruwan hawaye a gare ka. A haife ni a idonka, na rayu a saman kumatunka. In mace a saman laɓɓanka. Ina son ka, so mara misaltuwa.”


Idan ba a manta ba, a shekarar 2019 ce Adam A. Zango ya auri Safiya Chalawa, wanda hakan ya haifar da ce-ce-ku-ce kan zargin Jarumin yana auri-saki. Surutan sun taso ne ganin cewa ya auri mata da dama sun rabu kafin ita, wanda hakan ya sa ake tunanin ita ma ba za ta daɗe ba.


Kafin auren Safiya Challawa, Adamu ya auri mata biyar, amma duk sun rabu dasu. ga jerin sunayen matan da ya aura tun daga ta 1 har zuwa ta 6.


Amina ce matarsa ta farko kuma ita ce mahaifiyar ɗansa Haidar, sai Aisha ƴar Shika a Zariya wadda ta haifa masa ƴaƴa uku. Matarsa ta uku ita ce Maryam daga Jihar Nasarawa, sai ta huɗu Maryan AB Yola, wadda ta fito a fim ɗin Nas.


Matarsa ta biyar ita ce Ummukulsum wadda ƴar kasar Kamaru ce, kuma ita ce ta haifi  ƴarsa Murjanatu. Sai Safiya Chalawa, ta shida kuma ta haifa masa ƴa a bana.


Mutane da yawa suna masu sha'awar kallon fina-finan Kannywood suna yawan tsokaci game da auren da jarumi Adam A zango yake yi wanda baya zama da macen da ya aura. Hakan yasa wasu ke yi masa wata fassara daban cewa auren sha'awa yake yi.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post