Duk Namijin Da Ya Samu Mace Da Irin Wannan Halayen Zai Nace Har Sai Ya Aure TaHalaye da ɗabi'u na ƙwarai ke sa namiji yaji baya son ya rasa wacce yake son ya aura. Duk macen da take da waɗannan siffofin Maza na son su aure ta. Sai dai ba duka ne mata suke gane irin ɗabi'un da suke jawo hankalin maza zuwa gare su ba.


Shiyasa a wannan rubutun na yau muka kawo muku wasu daga cikin Waɗanan halayen da maza suke son suga duk macen da suke son yin rayuwa da ita ace tanada su. Sai dai ba duka mata ne suke da irin wannan siffofin ba, shiyasa muka yi wannan rubutun domin mata su koyi wannan halayen.


1: Macen da take da godiya duk ƙanƙantar kyauta da za'a yi mata. Ba duka mata ne ke nuna godiyar su ba idan anyi musu ƙaramar kyauta ba. Ita kyuta duk ƙanƙartarta idan anyi miki yana da kyau ki nuna farin cikin ki da murna tare da yin godiya ga wanda yai miki wannan Kyautar. 


Namiji yana son idan yaiwa macen da yake so kyauta ta nuna farin ciki da godiya. Wasu matan suna da raina kyuta, koda kuwa babbar kyauta ce. Babu namijin da zai so kasance da matar da take raina kyauta.


2: Macen da ba tada ɓoye-ɓoye. Ko nuƙ-nuƙu.

Wasu matan sukan ɓoye damuwar su ga mazajen da suke son auren su. Shi namiji yana son idan yana tare da macen da yake so tana faɗa masa damuwar ta. Kuma namiji baya son munafurci, yafi son duk abinda zaki karki ɓoye masa.


3: Tana nuna maka soyayya na gaskiya.

 Babu yaudara ko munafurci a tare da ita.

Wasu matan za su soka ne saboda ko kana da kuɗi ko wani abin duniya. Za ta nuna ma tana sonka bayan kuma a zuciyar ta ba haka bane. Akwai wasu samarin da take Soyayya dasu a ɓoye ba tare da sanin ka ba. Kuma idan namiji ya gano cewa ba shi kaɗai kike soyayya dashi ba to zai rabu dake ne gabaki ɗaya.


4: Wacce take da abun yi ba wacce batason yin komai ba kuma tana so ayi mata komai ko ta samu komai. 

Wasu matan ba su da wadatar zuci, basa yin ƙoƙarin su nemi na kansu, burin su kullum su ce ai musu. Irin Wannan matar sun riga sun kashe zuciyar su, babu wata sana'a da suka iya kuma baza su koya ba sai dai kawai a kawo musu. Maza basu son irin wannan matan. Duk irin arzikin da namiji yake dashi yana son yaga wacce yakeso bata dogara dashi ba gabaki ɗaya.

 

5; Macen da zata iya taimakamaka idan ka shiga halin rayuwa. 

Wasu matan suna da tausayi ga namijin da take so musamman idan yana cikin wani na damuwa ko rashin abin hannu, suna ƙoƙarin ganin sun taimaka maka da abinda zasu iya. Amma wasu matan idan suna tare da namiji idan ya shiga wani hali sai su rabu dashi. Duk namiji baya son kasancewa da irin wannan matan.


6: Macen da ta amince maka ta yarda da Kai. Duk namiji baya son zama da mace da take nuna rashin yadda akan sa. Mata masu yawan zargi akan mazajen su suna jawowa kansu ne, domin zama da zargin juna baya ɗorewa. Duk namiji yana son kasancewa da macen da ta amince masa ta yarda dashi.


7: Macen da ta take da Haƙuri.

Duk wani namiji yana son kasancewa da mace mai haƙuri, koda kuwa shi ɗin ba mai haƙuri bane, amma yana son yaga macen da yake tare da ita tana da haƙuri na zamantakewa. Duk abinda mace take taƙama dashi indai ba ta da haƙuri to akwai matsala babba domin duk wanda yake tare da ita ba zaiji daɗin rayuwa da ita ba.


8: Macen da take neman shawaranka:

Ba duka mata ne suke neman shawara ga namijin da suke tare dashi ba, kodai saurayi ko kuma miji. Sun fi ganewa cewa su nemi shawara daga wajen ƙawayen su, wanda kuma yawancin shawarar ƙawaye ba ta kawo mafita sai dai jefa ki ga halaka. Namiji yana son yaga wacce yake tare da ita budurwar sa ko kuma matar sa tana neman shawarar sa. Hakan yana nuna masa cewa ta yarda dashi.


9: Macen da take da Mafaɗa ( Masu yi mata faɗa ko tsawatar mata):

Wasu matan ko iyayen su ma basu iya faɗa musu magana su ji balle kuma saurayin su ko mijin su. Irin Wannan matan zaka same su ba su da kunya kuma basa jin kunyar kowa. Namiji yana so yaga mace mai jin magna da girmama manyan ta.


10: Mace mai kula da addininta.

Babban alfahari ga namji shine yaga ya samu mace mai riƙo da addini da tarbiyya. Hakan zai sa ƴaƴan da za ta haifa su taso cikin irin wannan ɗabi'ar. Sai dai ba duka ne ake samun mace mai yin riƙo da addini ba. Wasu mazan kafin su auri mace sai sun yi mata jarrabawa akan riƙo da addini da tarbiyyar ta. Domin samun mace mai addini da tarbiyya shine yafi komai.


Wannan sune daga cikin irin halayen da maza suke burin samun mace dasu domin yin rayuwar aure. Duk macen da take da irin wannan halayen zaka samu namiji ya nace akan ta sai ya aure ta. Da fatan mata wanda ba su da irin wannan siffofin za su yi ƙoƙari wajen ganin sun koya, wanda kuma suke da halayen su ƙara riƙe su da yin aiki da su.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post