Shugaban Ƙasar Nijer Bazoum Mohammed Ya Haramtawa Ministocin Sa Ƙara Aure


Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar, Mohammed Bazoum, ya haramta wa ministocinsa karin aure. Bazoum ya ce duk ministan da ke son yin ƙarin aure to ya sauka daga kujerarsa,  a wani mataki da shugaban ya ce zai taimaka wajen a rage yawan haihuwa barkatai a faɗin ƙasar.


“Na shaida wa ministocina cewa na haramta musu ƙarin aure, matuƙar suna cikin gwamnatina. Idan akwai ministan da ke son ya yi ƙarin aure ba za mu hana shi ba, amma kuma wajibi ne ya sauka daga muƙamin Gwamnatin Tarayya,” inji shi.


Ya sanar gargaɗin ne a wurin wani taron mata da aka gudanar a ranar 13 ga watan Mayu, a ƙasar, inda mahalarta suka yi ta sowa suna yabo. Sai dai kalaman nasa sun haifar da ce-ce-ku a Jamhuriyar Nijar, inda wani bangare yake ta caccakar shi a kan matakin da ya ɗauka na hana ƙara aure.


A lokacin da yake jawabin, shugaban ƙasar ya ce yawan al’ummar Jamhuriyar na ta ƙaruwa, ta yadda hakan ke barazana ga jin daɗin al’ummar ƙasar, bunƙasar masana’antu da kuma rayuwar yau da kullum.


Ya kuma nuna damuwa kan yadda ya ce maza ke ɗora wa mata nauyi, ta0ppp0re da buƙatar ɗaukar mataki kan irin halin da ke jefa su a cikin al’umma. 


Ko a shekarar da ta gabata ma sai da shugaban ƙasar yaja hankalin ma'aurata da su rage yawan haihuwa duba da yadda ake samun ƙaruwar yara wanda kuma ba'a iya kulawa da rayuwa su wanda hakan babbar barazana ce ga cigaban ƙasar.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post