'Ƴan sanda sun ceto mutum 100 da ƴan bindiga suka sace a Zamfara


Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya tace ta ceto mutum 100 da ƴan bindiga suka sace a yankin Dansadau da ke cikin karamar hukumar Maru jihar Zamfara.


KARANTA: Sakon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ga Yan Najeriya

KARANTA: Abubuwan Da Akeso Musulmai Suyi A Ranar Sallar Layya


Ƴan sandan sun ce mutanen sun shafe fiye da kwana 40 hannun ƴan bindagar kafin a ceto su a ranar Litinin ta hanyar sa bakin tubabbu da gwamnatin jihar ta yi sulhu da su.


Kakakin rundunar ƴan sandan SP Mohammed Shehu ya shaidawa Awwal Janyau cewa ƴan bindigar sun sace mutanen ne a ƙauyen Manawa ranar 8 ga watan Yunin da ya gabata, suka yi garkuwa da su a wani daji na Kabaru fiye da kwana 40. Bbc Hausa 


"Wannan ceto na daya daga cikin kokarin rundunar yan sandan jihar na ganin an kare rayuka da dukiyoyin jama'a.


"Tun lokacin da abin ya faru rundunar ta tashi tsaye da hadin gwiwar ma'aikatar tsaro da sauran masu ruwa da tsaki na al'umma da suke taimaka mana wajen samar da zaman lafiya.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post