APC za ta tsaida ɗan takarar shugaban ƙasa a sauƙaƙe ba sai an kai Ruwa Rana ba da zaɓen-fidda-gwani ba, Sakataren Jam’iyya
KARANTA: Ƴan sanda sun ceto mutum 100 da ƴan bindiga suka sace a Zamfara
KARANTA: Ga wani hadi na musamman domin mata
KARANTA: Har yanzu tsadar rayuwa na Wahalar da Marasa ƙarfi A Najeriya
Sakataren Riƙon Jam’iyyar APC ya bayyana cewa jam’iyyar ba za ta kai ga yin takarar fidda-gwani a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa na 2023 ba.
John Akponudoehede wanda shi ne Sakataren Riƙo na Ƙasa na APC ya bayyana hakan ne, a cikin wani martani da yayi wa PDP.
Sakataren ya ce tun a wurin taron Gangamin APC na Ƙasa da jam’iyyar ke sa ran shiryawa ne a ranar 31 Ga Agusta za a yi komai salum-alum, yadda kowa zai amince da wanda jam’iyya za ta tsaida.
“Idan cancanta za a bi maimakon zaɓe, to tilas wanda za a tsayar sai ya tabbatar ya na da cancantar da ake cewa ya na da ita ɗin.”
To sai dai kuma tun kafin ranar gangamin taron jam’iyyar APC ɗin, an fara samun ɓaraka a ɓangaren ‘yan takarar shugabancin APC na ƙasa.
Tsohon Gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari ya fara kartar-ƙasa ya na kirarin cewa babu wanda ya isa ya hana shi zama shugaban APC na ƙasa.