Nnamdi Kanu ya bayyana wa kotu dalilan da yasa ya gudu


Shugaban ƙungiyar 'yan taware IPOB, Nnamdi Kanu, ya bayyana dalilin da yasa ya fice daga Najeriya bayan an bada belin shi a shekarar 2017, kamar yadda Jaridar DailyTrust ta ruwaito. 


KARANTA: Yan bindiga sun kai farmaki tawagar Gwamnan Kano Ganduje

KARANTA: Yan bindigan da suka kashe Dan Majalisa a Zamfara sunyi garkuwa da dansa da direban sa

KARANTA: Abin Da ‘Yan Yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya Ke Cewa Kan Kama Nnamdi Kanu


Yace ya ɗauki matakin guduwa ne saboda an zagaye gidansa amma duk da haka sai da ya samu nasarar ficewa, kamar yadda premium times ta ruwaito. 


Kanu ya ƙara da cewa idan bai tsere ba, to za'a iya kashe shi kamar yadda ake yiwa sauran mambobin ƙungiyar IPOB. 


Alƙalin babbar kotun tarayya dake Abuja, Binta Nyako, itace ta bada belin Kanu bisa wasu dalilai na rashin lafiya a shekarar 2017. 


Alƙalin ta gargaɗi wanda ake ƙara da kada ya kuskura a ganshi a cikin taron mutum 10 ko kuma a ganshi a cikin wani gangamin taro. 


Amma duk da haka, Kanu ya tsallake waɗannan sharuɗɗan belin nasa, ya fice daga Najeriya, kuma daga can ya dinga umartan mambobin ƙungiyarsa. 


A ranar Talata, mai baiwa Antoni Janar Shawara, Shuaibu Labaran, ya shaida wa kotu cewa an damƙe Nnamdi Kanu kuma aka gabatar da shi gaban Kotu. 


Labaran ya roƙi kotun da ta bada umarnin a rufe shugaban IPOB ɗin da aka kama a hedkwatar hukumar tsaron DSS. 


Yace: "Muna roƙon kotu da ta bada umarnin tsare shugaban IPOB da aka kama a ofishin DSS." 


Alkali Nyako, ta ɗage sauraron ƙarar har sai ranar 26 ga watan Yuli za'a cigaba da gudanar da shari'ar.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post