Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kai farmaki tawagar Gwamnan Kano Ganduje'Yan Bindiga a Najeriya sun kai hari kan tawagar motocin Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje lokacin da ya ke barin Zamfara domin komawa gida abinda ya yi sanadiyar jikkata jami’an 'yan sanda guda 3 da ke rakiyar sa.


KARANTA: 'Yan bindigan da suka kashe Dan Majalisa a Zamfara sunyi garkuwa da dansa da direban sa

KARANTA: Cutar kanjamau gaskiya ce, ga alamomi 6 da mutum Zaiji a jikin sa idan ya kamu.

KARANTA: Illolin yin jima'i ta dubura ga lafiyar jiki


Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar Yan bindigar sun bude wuta akan jerin motocin Gwamnan ne bayan kammala taron Jam’iyyar APC da akayi a birnin Gusau inda Gwamna Bello Matawalle ya sauya sheka daga Jam’iyyar PDP.


Majiyar fadar gwamnatin Kano tace Gwamna Ganduje baya cikin motar sa lokacin da Yan bindigar suka bude wuta akan tawagar motocin.


Rahotanni sun ce Ganduje yabi tawagar Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar komawa gida, yayin da tawagar motocin sa suka bi shi.


Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da Yan bindigar suka harbe dan majalisar jihar Zamfara Mohammed Ali Ahmed dake wakiltar Shinkafi akan hanyar sa ta zuwa Funtua daga Gusau bayan kamala taron.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post