Meyasa ‘Yan Kudu Ba Sa Tada Fitina Sai Dan Arewa Na Mulki, Sheikh Balalau


An bayyana cewar tsagerun yankin Kudancin Najeriya ba sa tada hankali da kunna wutar fitinar a raba ƙasa sai ya zamana cewar ɗan Arewa ne ke kan shugabancin kasa.


KARANTA: Wata Mata Ta Yanke Azzakarin Mijinta Ta Soye Shi

KARANTA:  ‘Yar Aiki Ta Tsere Da Jaririn Gidan Da Take Aikatau A Kaduna.

KARANTA: Duk Gwamnan dake son Jiharsa ta Zauna Lafiya ya Koma APC, Gwamna Matawalle

 

Shugaban kungiyar Izala na ƙasa baki daya Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da aka yi dashi a ofishin Ƙungiyar dake birnin tarayya Abuja.


Sheikh Lau ya kara da cewar a duk lokacin da aka wayi gari ɗan Arewa musulmi na shugabancin kasa zaka tarar da jama’ar Kudu musanman yankin Inyamurai suna ta zuzuta wutar fitina da kaddamar da farmaki akan jama’ar Arewa da sunan batun wai a raba ƙasa.


“Shin ‘Yan arewa ne suka hana raba ƙasar, ko kuwa sai idan an kashe sune zai sanya a raba kasa? Wannan zalunci ne wanda ba za’a a yarda da shi ba”.


Shugaban Izalar ya cigaba da cewar akwai hanyoyi da dama da ake bi idan har batun raba kasa ya taso.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post