An Yankewa Masu Satar Mutane Hukuncin Daurin Rai Da Rai A Sokoto


Yadda aka yanke wa wasu masu satar mutane hukunci na ɗaurin rai da rai a jihar Sokoto.


KARANTA: Gwamnonin Kudancin Najeriya sun Ce Dole a ci gaba da karba-karba

KARANTA: Yan bindiga sun sace jarirai a Zaria

KARANTA: El-Rufai Ya Bada Umurnin Rufe Makarantu 13 a Kaduna Litinin,


Ƴan uwa da masu rajin kare haƙƙin ɗan adam sun bayyana ra'ayoyinsu a kan hukuncin ɗaurin rai-da-rai da Babbar Kotun Tarayya ta yanke wa wasu masu garkuwa da mutane huɗu a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya.


Kotun dai ta yanke musu wannan hukunci ne bayan ta same su da laifin garkuwa da wani fitaccen ɗan kasuwa a shekarar 2013, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa saboda jigata da ɗimautar da yayi.


Ba kasafai ake jin kotuna na yanke wa masu satar mutane hukunci irin wannan hukunci ba, musamman a yankin arewacin ƙasar, inda hare-haren ƴan fashin ke ƙara ta'azzara.


Duk da tsawon shekarun da aka kwashe bayan sace wa tare da yin garkuwa da marigayi Alhaji Abubakar Dankure, makusantan ɗan kasuwar sun ce ɗaurin rai-da-rai da kotu ta yanke wa masu garkuwar ya rage musu zafi da raɗaɗin aika-aikar da aka tafka musu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post