Gwamnatin jihar Kano ta sanya ranar da za'a fafata mukabala tsakanin fitaccen Malami Sheikh Abdul-Jabbar Nasiru Kabara da wasu Malamai na jihar.
Kwamishinan harkokin addinai na jihar Kano Muhammad Tahar Adamu wanda aka fi sani da 'Baba Impossible' ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a tattaunawarsa da yayi da sashen Radio BBC Hausa.
KARANTA: Meyasa ‘Yan Kudu Ba Sa Tada Fitina Sai Dan Arewa Na Mulki, Sheikh Balalau
KARANTA: An Yankewa Masu Satar Mutane Hukuncin Daurin Rai Da Rai A Sokoto
KARANTA: Wata Mata Ta Yanke Azzakarin Mijinta Ta Soye Shi
Ya ce za a gudanar da mukabalar ce ranar Asabar 10 ga watan nan na Yuli da muke ciki a Hukumar Shari'a da ke cikin birnin na Kano.
A cewarsa tuni ya mika takardar gayyatar yin mukabalar ga Malam Abdul-Jabbar da malaman da za su fafata da shi.
Kwamishinan ya bayyana haka ne kwanaki kadan bayan shugabannin zauren hadin kan malaman Kano sun zargi gwammatin jihar da "jan kafa" game da zaman tuhumar suka ce za su yi wa Sheikh Abduljabbar a kan zargin da ake yi masa na cin zarafin Manzon Allah (SAW) da Sahabbansa. Ya sha musanta wannan zargi.
A ranar Laraba ne wata Babbar kotun Kano ta amince da bukatar lauyoyi na Sheikh Abduljabbar kan sauraren hujojinsu na neman soke umarnin wata kotun Majistire da ke jihar na rufe masallaci da makarantar malamin.
Alkalin kotun, Mai shari'a Nura Sagir ne ya bayar da umarnin, bayan la'akari da korafin da malamin ya yi na rashin ba shi damar kare kansa daga wasu zarge-zargen da ake yi masa.
Da ma dai Sheikh AbdulJabbar ya bayyana dakatarwar da gwamanatin ta yi masa daga yin wa'azi da rufe masallacinsa da cewa "zalunci ne".