Mutumin Dake Auren Mata 39 Ya Mutu


Mutumin wanda ke arewa maso gabashin Indiya, wanda aka rawaito cewa ya fi yawan iyali a duniya, ya kwanta dama.


KARANTA: Gwamnatin Zamfara Ta Dakatar Da Sarkin Zurmi Kan Zargin Alaka Da 'Yan Ta'adda

KARANTA: Buhari Yayi Magana Kan Shirye-shiryensa Bayan Ya Sauka Daga Mulki A 2023

KARANTA: Wannan Hadin Na Amare Ne Zalla Da 'Yan Matan Da Zasuyi Aure


Ziona Chana wanda ke da kimanin shekaru 76. Iyalinsa sun ce ya yi fama da ciwon suga da hawan jini wanda yai sanadiyyar mutuwar sa.


Shidai Mista Chana yana da mata su 39 da kuma yara 94 da kuma jikoki da yawa.


Ya zauna ne tare da dukkanin iyalinsa a wani gidan bene mai hawa hudu dake a wani kauye mai tsaunuka a jihar Mizoram, da ke iyaka da Myanmar.


Jami'ai sun ce gidan ya zama wani babban wurin jan hankali ga 'yan yawon bude ido saboda yawan iyalin da mutumin yake dashi.


Mista Chana ya shugabanci wata kungiyar mabiya addinin Kirista da ke ba da damar auren mata fiye da daya.


Mista Chana Ya fara yin aure tun yana da shekara 17.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post