Har da tsohon Shugaban kasa Abdulsalam Abubakar kan zargin daukar nauyin ta'addanci"Abdulsalam yace Jama'a karku yarda da labarin da ake yadawa cewa an kama wani jirgin sama mai kaiwa 'yan bindiga abinci da makamai a jihar Neja mallaki na".


KARANTA: Mun Gano Mutanen DA Suke Daukar Nauyin Ta'addanci A Nijeriya, Inji Ministan Shari'a Malami

KARANTA:Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, azumi 30 za'ayi


Jaridar Muryar 'Yanci Tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar ya karyata labarin da ake yawo da shi cewa an cafke wani jirgin sama mai saukar ungulu wanda ake zargin yana kai wa 'yan bindiga kayan abinci da kuma kayan yaki a jihar Neja.

Abulsalam ya bayyana cewa "wannan labari ba gaskiya bane, sannan kada kowa ya yarda da wannan labari. Domin labari ne wanda aka kirkira don a bata min suna".

KARANTA: Mace mai haila zata iya yin kowace ibadah a watan Ramadan

KARANTA: Nayi jima'i a Ramadan, amma bazan iya kaffara ba, Ko zata fadi a kaina?

Tun jiya dai ne ake ci gaba da yada wannan labari wanda aka alakanta Abdulsalam da shi.


Daga karshe tsohon shugaban kasar ya roki Allah ya kawo wa ma Najeriya zaman mai dorewa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post