Real Madrid ta zubar da damar ta na lashe kofin Laliga


LaLiga: Real Madrid ta gamu da koma baya a kokarin ta na lashe kofin Laliga bayan da suka tashi 2-2 da SevillaKwallan da Eden Hazard ya zira a minti na 94 ya taimaka wa Real Madrid a wasan da suka tashi 2-2 da Sevilla a ranar Lahadi biyo bayan yanke hukunci mai ban mamaki da alkalin wasa ya dauka na bawa kungiyar Sevilla bugun daga kai sai mai tsaron raga wanda hakan ya sauya taken LaLiga cikin nasarar Atletico Madrid.

'Yan wasan Zinedine Zidane sun rama ta hannun Marco Asensio a tsakiyar rabin lokaci kuma suna tunanin suna da fanareti lokacin da aka saukar da Karim Benzema bayan da ya zagaye mai tsaron gidan Sevilla Yassine Bono.

Amma VAR ta sa alkalin wasa Juan Martinez Munuera ya duba kwallon Eder Militao da ya taba da hannu a 'yan sakanni kaɗan, da babbar shawara ganin an soke fenaritin Madrid kuma aka ba Sevilla bugun tazara.

Bayan wasan a yayin zantawa da manajan kungiyar ta Madrid, Zidane yace yayi matukar mamaki game da hukuncin da alkalin wasa ya dauka akan bugun daga kai sai mai tsaron raga da ya hanamu ya baiwa kungiyar ta Savilla. Yace abinda ke gabanmu shine wasan gaba domin zamuyi iya kokarin mu har zuwa karshen kakar.


Bayan da Barcelona da Atletico suka buga kunnen doki babu ci a ranar Asabar a Camp Nou, kashi na biyu na wasan hamayya tsakanin kungiyoyin biyu a karshen mako na LaLiga. A halin da ake ciki a yanzu Saman teburin bai canja ba yayin da wasanni uku suka rage a yanzu.

KARANTA: YANZU-YANZU: Sojoji sun kama wasu yan boko haram a Kano

Atletico ta ba Real Madrid da Barcelona tazarar maki biyu, yayin da take rike da kambun a hannunsu.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post