Mun Gano Mutanen DA Suke Daukar Nauyin Ta'addanci A Nijeriya, Inji Ministan Shari'a Malami



Mun Gano Mutanen DA Suke Daukar Nauyin Ta'addanci A Nijeriya, A Cewar Ministan Shari'a Abubakar Malami. 


KARANTA:Ba zai yiwu a ga wata ranar Talata a Najeriya ba, azumi 30 za'ayi


Ministan shari’a Abubakar Malami yace  binciken da suka gudanar ya nuna musu wasu fitattun 'yan Nijeriya da kuma 'yan kasuwar da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a cikin kasar.

Ministan ya ce tuni aka fara shirin gurfanar da wadannan mutane a gaban kotu domin fuskantar shari’a akan rawar da su ke takawa wajen haifar da tashin hankali, sakamakon binciken da gwamnati ta gudanar a Daular Larabawa dangane da masu daukar nauyin bai wa boko haram kudade.

Wannan matakin na gwamnati na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasar ke fuskantar karuwar hare-haren ayyukan ta’addanci na boko haram a yankin arewa maso gabas da kuma wasu hare-haren na daban a wasu yankunan kasar. 

KARANTA:Ainihin dalilin da ya sa Buhari ya dakatad da Hadiza Bala Usman


Malami ya ce gwamnati ta dauki dogon lokaci ta na gudanar da bincike akan wannan lamarin da ya shafi ayyukan ta’addanci bayan da kotu a Daular Larabawa ta daure wasu 'yan Nijeriyar guda shida.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post