Banyi bude baki ba na Sadu da Matata, ya matsayin Azumi na yake?YA YI BUDA BAKI DA JIMA'I DA MATARSA?


KARANTA:Mahaifiyata ta Rasu Ana binta Azumi, Shin Zamu iya rama mata?

KARANTA:Ko Kunsan Ranar da ake neman Lailatul Qadri, karanta karin bayani


Tambaya

Aslaam alaykum mlm barka da warhaka dafatar kana lapia. malam minene hukuncin Wanda yayi azumi amma bai yi buda baki ba, ma'ana bai sha ruwa bayan ladan ya kira sallah. Sai yayi jima'i da matarsa, Ya azuminsa?.


Amsa

Wa alaikum assalam, Azuminsa ya yi daidai, mutukar ya sadu da ita ne bayan rana ta fadi.                       


Annabi ﷺ ya yi umarni ayi buda baki da dabino ga wanda ya samu dama, in ba hali kuma ayi da ruwa kamar yadda ya tabbata a hadisai.                                                                                                      

Abin da ya gabata yana nuna cewa: 

Yin buda baki da dabino ko ruwa shi ne sunna, saidai wanda ya fara da jima'i azuminsa ya inganta, tun da Allah ya halatta masa jima'i a daidai wannan lokacin kamar yadda aya ta: 187 a suratul Bakara ta nuna hakan.

                                                                 

Allah ne mafi sani.Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post