Mahaifiyata ta Rasu Ana binta Azumi, Shin Zamu iya rama mata?


Mahaifiyata ta Rasu Ana binta Azumi, shin zamu iya rama mata?


 Tambaya

Assalam Alaikum warahmatullah wabarakatuh! 

Malam dan Allah ina da tambaya: tun kafin a kama azumi uwata bata da lafiya har akayi sallah, rana ta 16 ga watan karamar sallah  Allah yayi mata rasuwa, shin za mu rama mata azumi ko ba sai mun rama mata ba? Allah ya saka da hairi.


KARANTA:Ko Kunsan Ranar da ake neman Lailatul Qadri, karanta karin bayani

KARANTA:Kada Ka Sake Cin Gyada Idan Ka Lura Da Waɗannan Abubuwan A Jikinka!


  Amsa                    

Wa'alaikumus Salam warahmatullah wabarakatuh!  

To malam mutukar rashin lafiyar ta zarce mata, har zuwa lokacin mutuwarta, to ba za ku rama mata ba, tunda ba sakaci ta yi ba, saboda fadin Allah madaukaki: "Kuma duk wanda yake mara lafiya ko matafiyi to sai ya rama a kwanaki na daban" Bakara aya ta: 185, wato bayan Ramadahana, idan mara lafiya ya samu sauki, ko matafiyi ya dawo , Ka ga wanda bai samu sauki ba har ya mutu, zai zama bai kai lokacin da zai rama ba, don haka sai ya saraya akan shi.

Amma idan ta samu damar ramawa, ta yi sakaci ba ta rama ba har ta  mutu, to sai makusancinta ya rama mata, saboda fadin Annabi ﷺ: "Duk wanda ya mutu akwai azumi akansa, to sai makusancinsa ya rama masa". Kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta: 1851.

Duba Fataawa nuru aladdarb lamba ta: 247.


Allah ne mafi sani



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post