WANNAN HADIN SHINE AKE KIRA DA HADIN YAR GATA

 



HADIN 'YAR GATA(KI GYARA DA KANKI)

Wannan hadin anyi shine kyauta domin amfanin iyayen mu mata, Kanne, yayye da dukkan sauran mata da suke da bukata.

 Shi dai wannan hadin bashi da wani wahalar hadawa kuma abubuwan da ake hadin dasu basuda wahalar samu a duk inda kike zaki same su. 

Shi dai wannan hadin duk macen da take yinsa zai Kara mata lafiya, ni'ima, dan-dano, kuzari da gyaran jiki. 


- Idan kina shan ruwan kubewa mijinki bazai taba kaurace Miki ba


Abubuwan da zaki bukata sune Kamar haka:

(1) Gyada Kofi 1

(2) Aya Kofi 1

(3) Cikwi faifai daya(wanda akeyi da nonon rakumi)

(4) Dabino gwangwani daya

(5) Ridi rabin cup (kantu)

(6) Mazarkwaila rabin faifai.

Karin bayani idan zaki samo wadannan kayan hadin da muka lissafa. 

  • Cikwi, yana zuwa a fai-fai, da manya da kanana, idan manya ne rabin fai-fai ya isheki, idan karami ne sai ki samu fai-fai daya, kuma wani lokacin ba bausashe bane, dan haka idan kin siya zaki babballa shi ki busar ya bushe sosai.


  • Aya, zaki wanke ki rege dan ki fitar da dukkan datti da tsakuwa, sai ki baza ta bushe sosai.


  • Gyada zaki sayi cup 1(wato gwangwani daya) ki tsince ki fitar da duk wani datti, sai ki zuba a frying pan ki kunna wuta, ita kadai babu mai babu ruwa, zaki ringa juyawa, sai ki sauke ki saka hannayenki ki murtsuka ta zaki ga brown bayan sun fita tas, kuma hakan zaisa ta bushe.


  • Mazarkwaila, itama a fai-fai take zuwa, ana yinta daga rake kai tsaye, sai ki samu rabin fai-fai ki ajiye.


  • Dabino, zaki samu cup daya(gwangwani daya), idan ba busashe bane to sai ki bare shi ki fitar da kwallon ki shanya shi ya bushe.


  • Ridi, zaki samu ridi(Soyayye) rabin cup (rabin gwangwani).

Bayan duk kinsamu wannan kayan da muka lissafa Zaki hada su duka ki dake su sosai su zama gari. Amma wasu daga ciki daban-daban zaki dake ba ina nufin ki hade su waje daya ki dake ba, sai ki hade garin gaba daya ki samu container mai murfi ki rufe, idan kin tashi amfani sai ki bude ki diba, bazai lalace miki ba har  zuwa tsawon watanni 2, idan har komai busashe ne babu danshi.


Kayan da zakiyi wannan hadin dashi 

Zaki samu madarar ruwa ko yoghurt/nono mara tsami da zaki ki ringa hadawa kina damawa kina sha.


Zaki iya diban garin da kika hada, ki zuba masa madara/yoghurt ki ringa sha tsawon kwana 5-7 zaki sha mamaki.


Amfanin wanan hadi dan gyaran jiki na Amarya da Uwar gida, dan kauda duk wata matsalar bushewa da rashin ingantacciyar lafiya a jikin mace.




Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post