KO KUNSAN WAYE CIKAKKEN NAMIJI A CIKIN MAZA?

 



CIKAKKEN NAMIJI ACIKIN MAZA


Assalam Alaikum warahmatullah wabarakatuh! Barkanmu da sake saduwa daku a wannan lokacin a cikin cigaba da shirye_shiryen mu. A yau insha Allah zakuji wasu halaye na cikakken namiji wanda ya fita dabam a cikin mazaje. 

Maza kala kala ne, akwai waɗanda suke amsa sunan su na mazaje akwai kuma waɗanda suke basa amsa wannan sunan a gurin matayensa. Wannan alamu na cikakken namiji sune Kamar :


  • Cikakken namiji wanda yasan ƙiyamah da darajar matarsa, shine wanda yake damuwa da damuwar ta, yake kwantar mata da hankali a lokacin da take tsaka da damuwa, wanda yake faranta mata rai a lokacin da ranta ya ɓaci. 


  • Shine wanda yake nuna tsantsar soyayya da kulawarsa ga matarsa, wanda baya taɓa hantara ko zagi da cin mutuncin ta ko zagin danginta, shine wanda yasan dukkanin ilahirin haƙƙin ta wanda yake akansa kuma yake ƙoƙarin sauke shi domin ya faranta mata rai kuma ya yiwa ubangijinsa biyayya a cikin sauke haƙƙin da ya rataya a wuyansa na aure. 


  • Cikakken namiji kuma gwarzo a cikin mazaje, shine wanda yake ɗaukar matarsa a matsayin abokiyar rayuwarsa, wacce suke mutunta juna a tsakãninsu, shaiɗan baya nasara acikin zamantakewar rayuwar aurensu, zargi baya shiga tsakaninsu, kullum saidai batun girmama juna da kuma ganin mutuncin juna. 


  • Cikakken namiji bashi bane mai yawan dukan matarsa ba, kuma bashi bane mai yawan zagin ta ba, cikakken namji shine mai yawan furta albarka akan matarsa, mai yawan ambaton ta da alkhairi, baya taɓa yarda ya furta mummunar magana game da ita, yana kare mata ƙima da darajarta a duk inda ya tsinci kansa, baya tozarta ta a gaban abokansa ko sauran mutane. 


  • Dukkanin namijin da bai iya biyan buƙatun iyalansa na yau da kullum ba, to lallai wannan ba cikakken namiji bane, kasancewar ka cikakken namiji, yana farawa ne daga lokacin da ka iya ɗaukewa iyalanka dukkanin nauyinsu wanda ya rataya a wuyanka, kullum burinka ya zamto cewa ka kyautata musu ne, ka yalwata musu, ka kangesu daga haram


  • Yana daga cikin siffar cikakken namiji, shine wanda ya iya kare mutuncin gidansa, wanda yake kare tarbiyyar iyalansa, tun daga kan matayensa na aure har izuwa kan ƴaƴansa, matuƙar namji bai basu kyakkyawar tarbiyya ba, to lallai haƙiƙa wannan ba cikakken namji bane, domin lallai ya bari gidansa yafi ƙarfinsa, sabida ita tarbiyya daga gida take farawa, to shi kuma yayi sake da ta iyalansa


Ka kasance mai yawan tarairayar matarka ba wai mai yawan hantararta ba, itama tanada haƙƙi akanka, sannan ko babu komai ai ita matattarar sirrikan ka ce, sabida haka kada ka sake ka tozarta ta a rayuwar auren ku. 

Allah ya bawa maza Ikon kula da hakkin matayen su, su ma matan Allah ya basu Ikon kula da mazajen su bisa gaskiya da rikon amana amen.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post