LOKUTAN DA AKE KARBAR ADDU'A RANAR JUMA'A


KU LALUBI LOKACIN KARBAN ADDU'A RANAR JUMA'A


Shaykh Ibnu Baaz(RA) ya ce:


Ubangiji ya sanya wata sa'a a ranar juma'a wanda ya ke karban addu'a a cikinta, lokaci ne kadan wanda babu wani musulmi da zai dace da ita yana tsaye yana sallah face Allah ya bashi abin da ya roka, don haka lokaci ne mai girma kuma bashida tsawo.


(1) Ya zo a wasu ruwayoyin cewa lokacin shine sanda liman ya zauna a kan minbari zuwa a idar da sallah.


(2) Ya zo kuma cewa lokacin yana a tsakanin Sallar La'asar zuwa faduwar rana.


Naci abinci bayan alfijir ya keto ya matsayin azumi na?

Bambancin maniyyin namiji da maniyyin mace


(3) Ya zo a wasu hadisan cewa lokacin shine sa'ar karshe na ranar juma'a


Wadannan sune lokutan da a ka fi tsammanin wannan sa'a, haka sauran lokutan juma'a gaba daya a na fatan a amsa addu'a a cikinsu.

Don haka ya kamata musulmi ya yawaita addu'oi a ranar juma'a don fatan dacewa da wannan sa'ar, kuma yana kyau ya ribaci wadancan lokuta ukun da a ka ambata a sama ya ba su karin kulawa domin Manzon Allah(SAW) ya nassanta cewa shine lokacin amsar addu'a.


مجموع  فتاوى ومقالات الشيخ ابن باز 197/25



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post