FALALAR YIN SAMMAKO ZUWA SALLAH JUMU'A

 



FALALAN SAMMAKO ZUWA JUMU'A 

             

Daga Sahabi Abi Umamata cewa;  Manzon Allah (SAW) yace; Mala'iku suna zama ranan Juma'a a kofofin masallaci, a tare dasu akwai wasu takardu suna rubuta sunayen mutane, idan liman ya fito, se su nad'e takardu, se nace, Ya Aba Umamata, Kenan babu ga Wanda yazo bayan zuwan Liman (ma'ana bashi da juma'a?) Se Abi Umamata yace;  a'ah!  Se dai bai zamo ba daga cikin wanda aka rubuta a cikin wancan rubutun.


 Imam Ahmad, kuma Al-baniy ya ingantashi


Karin bayani:

  •  Wannan falalan shima na masu sammako ne (zuwa da wuri kafin zuwan Liman)


  •  Idan kazo bayan zuwan Liman (lokacin da ake huduba) kaima kana da juma'a, se dai baka da wancan falalan na rubuta sunaye da Mala'iku suka yi. Duk abinda Allah Ta'ala kuma ya yi akwai hikima a cikin sa.


Allah Ta'ala ya bamu ikon sammako zuwa sallah Juma'a amen.

Dan Allah ku turawa sauran al'umma domin tunatarwa, Allah ya hadamu a ladan gaba daya amen. 



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post