HIKIMOMIN DA AZUMI YA KUNSA

 



HIKIMOMIN DA AZUMI YA KUNSA


Tambaya:

Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuh! 

Don Allah malam a taimaka min da bayani game da sababin da yasa ake yin azumi?? 



 Amsa:

Amen Wa'alaikum assalam warahmatullah wabarakatuh! 

Azumi ginshiki ne, daga cikin turakun musulunci, wadanda addinin musulunci, ba zai cika ba sai da su, Allah da manzonsa sun yi umarni da shi, saboda wasu muhimman manufofi, ga wasu daga ciki: 


(1) Samun tsoron Allah, saboda mai azumi yana barin abin da yake so saboda Allah, hakan zai sa, ya kara samun tsoron Allah.


(2) Samun kariya daga Shaidan, saboda azumi yana takure hanyoyin Shaidan, wannan ya sa zunubai suke karanci a Ramadan.


(3) Tuna talakawa da wahalar da suke ciki, saboda duk lokacin da mai kudi ya dandana yunwa zai tuna halin da talakawa suke ciki.


(4) Sabawa rai wajen barin abin da take so, da kuma hakuri akan abin da take sha'awa.


(5) Kankare zunubai da kuma samun daukakar daraja, saboda azumi yana gyara zuciya, da kuma rai.


(6)Samun lafiyar jiki, saboda azumi yana kariya daga cututtuka masu yawa, kamar yadda likitoci suka tabbatar da hakan.


(7) Ta hanyar azumi mutum zai saba da yin aikin don Allah, saboda azumi sirri ne tsakanin Allah da bawansa.


Allah ne mafi sani. 

Ayi share zuwa social media domin al'umma su amfana. 



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post