MAGANIN INFECTION SADIDANMAGANIN INFECTION SADIDAN

Idan mace tana fama da kaikayi ko kuraje ko fitar farin ruwa mai wari, bushewa, daukewa, budewa, kwailewa da rashin sha'awa ko gamsuwa da sauran cututtukan sanyi, sai a gwada daya daga cikin wadannan hanyoyi.

(1)A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya.Yana maganin budewa da kaikayi.

(2) A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa,

Sai mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma.

Yana fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari.

(3) A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono ana sha.

Yana magance matsalar ruwan infection.

(4) A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma.

Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba.

(5) A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha.

Wannan yana mganin rashin sha'awa da bushewa da rashin gamsuwa.

(6) A dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a dama, a tace, a yi lemon juice da shi.

Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma yana kara ni'ima.

(7) A samu `Dan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki.

Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga shigarta.

Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna.

Zai magance mata kaikayi da kuraje kuma yana sa matsewa.

(8)A samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barkono da Raihatul Hubbi,

sai ta dake su tayi Yaji ta dinga cin abinci da shi.

Yana saukar da ni'ima da magance duk

matasalolin sanyi.

(9)A samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka su.

A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a tankade.

Sai a zuba akan sabulan da aka daka sannan a kwa6a da Ma'ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski.

Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau daya. Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu yana maganin kuraje da kaikayi da fitar wari.

(10) A samu Man Zaitun da Man Habba da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hadesu waje daya.

Mace ta dinga shan cokali daya kullum kafin ta karya.

Yana wanke dattin mara kuma yana samar da ni'ima.

(11) A samu Ciyawar Kashe-Zaqi da Farin Magani sai ta hada waje daya ta dinga jika rabin karamin cokali tana sha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali daya kullum kafin ta karya.

Wannan yana maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa.

ABUBUWAN DA SUKE KAWOWA MATA CIWON SANYI KO INFECTION.

 • Rashin sanya pant.
 • Barin pant yayi dauda sosai ba a canja ba. Ana so in da hali kullum a canja pant sau biyu a wanke.
 • Saka pant a jiqe da ruwa.
 • Yawan tsarki da ruwan sanyi.
 • Yawan tsarki da ruwan da zafinsa yayi yawa.
 • Rashin aski.
 • Wasa da gaba.
 • Yawan cin `Danyar Albasa.
 • Yin amfani da Magungunan mata marasa inganci.
 • Dadewa akan Masai ko toilet.
 • Rashin shan iska.
 • Musanyar tufafi.
 • Saduwa da mai cutar.
 • Cutar Aljanu, wato
 • Jinnul Ashiq. Su ma suna sanyawa mace infection mai wuyar magani.

ILLOLIN DA SANYI KO INFECTION YAKE YI WA MATA

 • Yana sa Rashin Sha'awa.
 • Yana sa ciwon mara mai tsanani.
 • Yana haifar da kurajen bakin mahaifa ko ya toshe mahaifar baki daya.
 • Yana sa mace ta dinga jinin al'ada baki kirin mai wari.
 • Yana sanya farin ruwa mai wari ya dinga fito mata.
 • Yana sanyawa a dinga jin mace tana wari mara dadi kuma a rasa ta ina yake fitowa duk wankanta.
 • Yana sa jin zafi yayin saduwar aure ko kuma ganin jini a maimakon ruwa.
 • Yana rikitawa mace kwanakin al'adarta, su dinga karuwa ko raguwa ko jinin ya dinga wasa.
 • Yana sanyawa mace tusar gaba, wato iska ta dinga fita ta gabanta.
 • Yana sanyawa mace yawan `Barin ciki ko kuma rashin shigar cikin kwata-kwata. Idan yayi karfi yana hana mace haihuwa.
 •  Wani infection din alama ce ta zaman Aljanu a jikin mace, musamman idan tana mafarkin namiji dare ko jarirai.

Abin lura:-

Idan mace tayi magungunan Asibiti

da kuma irin wadannan da mu ka ambata amma infection din bai warke ba, To ta nemi maganin jinnul Ashiq, wato magungunan Aljanu don zai iya yiwuwa matsalarsu ce.

Ina rokon dan Allah duk wanda yakaranta wannan post to yayi share dinshi domin kararuwar yan uwa musulmai. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post