MATA KU SAURARA KADA KU BARI A RUDEKU

 


MATA KU SAURARA KADA KU BARI A RUDEKU


     Sheik Saleh bn Fauzan bn Abdullahil Fauzan yana cewa:


    "Yanzu da musulunci yayi wa mata gata na 'karshe, ya cire su daga cikin 'Kangi na rayuwa. Sai ga wasu makiya addinin Allah karara sun bayyana suna neman karkatar da wasu daga cikin matan musulmai masu son zuciya da rashin godiya zuwa wasu wulakantattun zantuka/al'amura da sunan 'yanci da cigaba. 

     Waennan masu bakin ciki da hakkoki masu daraja da aka baima Mata, sai suka bullo da hanyoyi daban-daban dan ganin sun watsar da wannan darajar da 'yancin. Suka dorasu akan tsarin dai-daituwa da maza bayan Allah Ya riga da Ya Sanya wannan fifikon a tsakani. Suna inkari da hukuncin Allah, amma a haka saida aka samu gurbatattun musulmai da suka goya musu baya suka kuma yi riko da wannan mummunar hanyar.

     Duk yadda zaayi suga sun zubar da daraja da mutuncu da musulunci ya baiwa mata shi suka sa a gaba.  

Sun mayar da Mata ababen tallata hajarsu. Zaka ka hutunan Mata ajikin kwali na sabulai, posters da ma akwatunan talebijin da sauransu. Sune masu jawo musu customers da muryoyinsu, kyawunsu, surarsu da ma basirorin da Allah Ya basu irin haka yana faruwa acikin kamfanoni, jirage, bankuna da sauransu.

    Aka kuma dorasu akan harkar film da sunan fadakarwa da kuma sana'a. Babban burinsu, su dinga gwamuza maza da Mata a wajan mu'amala ta yadda za a cigaba da yada fasadi a bayan kasa. 

   Bukatarsu su fitar da mattattaki daga gidajensu, su cire musu kwadayin hidimomi na mazajensu, 'ya'yansu dama gidajensu baki daya. Hakkokin da musulunci ya tanadar wa Mata akan mazajensu da 'ya'yansu sun zama abun ko oho ga wasu matattakin wannan lokaci.

    Wasu matan dan tsabar rashin kishin kai da addinin su sun zabi barin kulawar mazajensu da 'ya'yayensu dama gidajensu baki daya a hannun 'yar aiki. Su kuma sun shiga gari neman duniya. Ba tare da tunanin hakkokin da Allah zai tambayesu akai ba."


Ku farka Mata! Waennan mutane makiyane gareku, jagororin shaidan ne. 


 📖 تنبيهات على أحكام التختص بالمؤمنات Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post