YADDA AKE SO A GUDANAR DA SALLAH JANA'IZA


TAƘAITATTUN BAYANAI AKAN NAU'UKA NA SALLAH NAFILA 6


1 1 SALLAR JANA'IZA 

    Haƙiƙa musulunci addinine mai cike da rahama da tausayin mabiyansa ahalin suna raye dama lokacin da suka mutu, alokacin da rai ya fita daga jikin gangan jikin mutum hakika awannan lokacin bawa yanada matsananciyar ceto da rahama na ubangijinsa hakan yasa musulunci ya shar'anta ayi masa sallah, wanda wannan sallah cike take da nema masa gafara da rahama wurin ubangijinsa.

    HUKUNCIN SALLAR JANA'IZA 

  Babu sabani na malamai akan cewa yin sallar jana'iza fardhu kifayane (idan wasu sukayi ta faɗi akan sauran) amma saboda hikima ta musulunci sai ya sanya lada mai tarin yawa ga duk wanda ya hakarci sallar saboda mai hankali ya tilastawa kansa zuwa ko dan samun wannan tagonashi. Dalili akan cewa fardhu kifaya ne shine; Hadisin Sahabi Khalid bin Zaid Aljuhani Allah ya ƙara masa yarda yace wani mutum daga cikin sahabban manzon Allah ya rasu, sai akazo aka labartawa manzon Allah, sai yace "Kuje kuyiwa abokinku sallah" sai fuskar sahabbai ta sanja, da manzon Allah yaga haka sai yace "Abokinku yayi gululi ne (ya dauki wani abu daga cikin ganima kafin araba)..."

     أبو داود ٢٧١٠

Wannan hadisin yana nuna mana cewa sallar jana'iza fardhu kifaya ne domin da fardhu Ainin ne da manzon Allah ya masa sallah.

    FALALAR SALLAN JANA'IZA 

   Amir bin Sa'ad bin Abi Waqqas yazo wurin Abdullah bin Umar suna zaune sai Khabbab ya leko wurinsu yake cewa ya kai Abdullah shin kaji abunda Abu huraira yake cewa?? Yana cewa yaji manzon Allah yace "Duk wanda ya fita tare da gawa daga gidanta, aka mata sallah tare dashi, sannan ya bita har zuwa maƙabarta aka bunneta yanada qiraɗan guda biyu na lada, kowane qiraɗi kuma ya kai girman dutsen uhud, wanda kuma yayi mata sallah kawai ya koma bai bita maƙabarta ba to yanada lada kamar dutsen uhud"?? Sai Ibnu Umar ya cewa Khabbab kaje wurin Nana Aisha ka tambayo mana ita duk abunda ta gayamaka kazo ka gayamin, shikuma Ibnu Umar ya zauna acikin masallacin ya ɗebi ƙasa ahannunsa yana jujjuyawa yana jiran khabbab, bayan khabbab ya dawo sai yace masa Nana Aisha tace "Abunda Abu Huraira ya faɗa gaskiya ne" Sai Ibnu Umar ya buga wannan ƙasar da yake ya hannunsa yace lalle munyi asarar quraɗi masu yawa".

 صحيح البخاري ١٣٢٥ 

          JAM'I A SALLAN JANA'IZA

  Yin jam'i a sallar jana'iza wajibine saboda dawwamar manzon Allah akan aikata hakan, da kuma faɗinsa da yayi "Kuyi sallah kamar yadda kukaga ina sallah".

      Sannan anaso adadin mutanen da zasuyi jam'in ya kai mutane 40, saboda hadisin Kuraib yace watarana Ɗan Abdullah bin Abbas ya rasu a qadeed ko Asfaan, sai ya cewa Kuraib fita ka duba mutane sun haɗu, da ya fita yaga sun haɗu sai ya gayamasa, sai Ibnu Abbas yace masa kanaga zasu kai Arba'in?? Sai yace eh, sai Ibnu Abbas yace afito da mamacin, domin lalle ni naji manzon Allah na cewa "Babu wani musulmi da zai mutu asamu mutane 40 su masa sallah waɗanda basa shirka ga Allah face Allah ya basu cetonsa"

 صحيح مسلم ٩٤٨

 Haka kuma idan sun kai ɗari suma Allah zai basu cetonsa, kamar yadda yazo ahadisin Nana Aisha Allah ya ƙara mata yarda take cewa manzon Allah yace "Babu wani da zai mutu asamu musulmai da suka kai ɗari su masa sallah kowannensu yana nema masa ceto face sun sama masa ceton"

 صحيح مسلم ٩٤٧

     Sannan kuma anaso masuyin sallan suyi sahu aƙalla guda uku, yazo acikin hadisin Malik bin Hubaira yana cewa naji manzon Allah yana cewa "Babu wani musulmi da zai mutu asamu sahu na musulmai guda uku su masa sallah face ta wajaba agareshi". Malik ya kasance idan mutane sukayi ƙaranci awurin jana'iza sai ya rabasu sahu uku saboda wannan hadisin".

 سنن الترمذي ١٠٢٨


   MATSAYAR LIMAN YAYIN SALLAN JANA'IZA

Idan mamacin namijine to liman zai tsaya adaidai kansa ne, amma idan macece to liman zai tsayane adaidai tsakiyar ta, dalili akan haka kuwa shine Hadisin Abu Ghalib yake cewa nayi sallan gawa tareda Anas bin Malik gawan namiji sai ya tsaya adaidai kansa, sannan sai aka kawo gawar wata mata daga quraish sai sukace ya Aba Hamza ka mata sallah, sai ya tsaya adaidai tsakiyarta, sai Ala'u bin Zayyad yace masa "Haka kaga Annabi (SWA) yai yace na'am. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post