TAƘAITATTUN BAYANAI AKAN NAU'UKA NA SALLAH NAFILA

 


TAƘAITATTUN BAYANAI AKAN NAU'UKA NA SALLAH NAFILA 3


0 5 SALLAR TUBA

   Haƙiƙa Allah shine mai gafara da yafiya ga bayinsa, babu wani laifi da bawa zai aikata ya nemi tubar Allah da yafiyarsa face Allah ya gafarta masa wannan laifin, Rahamar Allah bata tsaya akan iya gafarta masa da yafe masa ba kawai, a'a Allah zai mayar masa da wannan laifin ya zama lada, kamar yadda Allah ya fada acikin Alqur'ani mai girma, Surah Alfur'qan, Aya ta 70

  'Sai dai waɗanda suka tuba suka kuma aikata aiki mai kyau, waɗannan sune wanda Allah zai musanyar da aikinsu na laifi izuwa ga lada, lalle Allah ya kasance mai gafara ne mai kuma jin ƙai". 

    Abisa wannan dalili Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya shar'anta yin Sallar tuba ga duk wanda ya aikata wani zunubi da yakeso ya tuba akai.

     Sahabi Aliyu bin Abi Ɗalib Allah ya ƙara masa yarda yake cewa Ni mutum ne da idan naji hadisi daga manzon Allah to Allah na bani ikon yin amfani dashi, idan kuma wanine daga cikin sahabbai ya bani labari ina neman ya rantse akan cewa yaji manzon Allah ya faɗa, idan ya rantse sai ingasƙata shi in karbi hadisin, watarana Abubakar sadiq Allah ya ƙara masa yarda ya bani labari kuma na gasƙata shi, yace naji manzon Allah yace "Babu wani mutum da zai aikata wani zunubi, sannan ya tashi yayi tsarki yayi sallah sannan ya nemi gafarar Allah face Allah ya gafarta masa" sannan sai ya karanta wannan ayar ta cikin surah Ali Imran aya ta 135 "kuma sune waɗanda idan sun aikata wata alfasha ko suka zalunci kansu suke tuna Allah sai su nemi gafarar zunubansu, waye mai gafarta zunubai inba Allah ba, sannan basa dogewa akan abunda suka aikata na laifi alhali suna sane"

صحيح سنن الترمذي ١/١٢٨


0 6 TAHIYATU MASJID

     Wannan sallah ta tahiyatul masjid Sallace da akeyinta aduk lokacin da mutum ya shiga masallaci kafin ya zauna zai yita, raka'a biyu sauƙaƙa batare da tsawaitawa ba.


 HUKUNCIN TA

 Wannan sallah wajiba ce akan duk musulmin da ya shiga masallaci kafin ya zauna tilas yayisu, dalili akan haka kuwa shine; Hadisin Sahabi Abu Qatada Allah ya ƙara masa yarda yace manzon Allah yace "Idan ɗayanku ya shiga masallaci kada ya zauna har sai yayi raka'a guda biyu". Awata ruwaya kuma yake cewa "Idan ɗayanku ya shiga masallaci kada ya zauna har sai yayi sallah" 

   صحيح البخاري ٤٤٤

IDAN YA SHIGA MASALLACI YA SAMU ANTAYAR DA SALLAH 

    Alokacin da mutum ya shiga masallaci ya tarar da an tada sallah to bazaiyi tahiyatul masjid ba, zai shiga sahune kawai yabi liman tahiyatul masjid ta faɗi akansa, dalili kuwa shine Hadisin Abu Huraira Allah ya ƙara masa yarda yana cewa Manzon Allah yace "Idan aka tsayar da sallah to babu wata sallah sai ta farillah"

صحيح مسلم ٧١٠

 IDAN KUMA YA SAMU LIMAN NA KHUDBA

    Idan mutum ya shiga masallaci sai ya samu liman yana khudba na juma'a to bazai zauna ba har sai yayi sallah raka'a biyu, tahiyatul masjid, dalili akan haka kuwa; Hadisin Jabir bin Abdillah Allah ya ƙara masa yarda yake cewa Sahabi Saleek Al-Ghaɗfani ya shigo masallaci ranar juma'a manzon Allah yana khudba sai ya zauna, sai manzon Allah yace masa "Ya kai saleek tashi kayi sallah raka'a biyu amma ka tsagaita su" sannan sai manzon Allah yace "Idan ɗayanku yazo masallaci ranan juma'a ya tarar da liman na khudba to yayi raka'a biyu ya kuma tsagaita acikinsu kada ya tsawaita".

صحيح البخاري ٩٣٠


Mu haɗu adarasi na gaba inda zamu dora akan nafilar juma'a da kuma ta dawowa daga tafiya in sha Allah.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post