FALALAN BIYAN BUKATAUN MUTANE DAGA BAKIN ANNABI (SAW). .



FALALAN BIYAN BUKATAUN MUTANE DAGA BAKIN ANNABI (SAW).

GABATARWA

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa 

.

NA FARKO (1)-

ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ

ﻣﻦ ﻳﻜﻦ ﻓﻲ ﺣﺎﺟﺔ ﺃﺧﻴﻪ ﻳﻜﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﺣﺎﺟﺘﻪ .

( ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ )

Manzon Allah (saw) Yace:-

Duk Wanda Ya kasance Cikin Biyan Buqatar Dan Uwansa, Allah Zai Kasance Cikin Biyan Buqatar Sa

.

NA BIYU (2)-

* ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ

ﻭﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﻋﻮﻥ ﺍﻟﻌﺒﺪ ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻌﺒﺪ ﻓﻲ ﻋﻮﻥ ﺃﺧﻴﻪ،

‏( ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ )

Manzon Allah (saw) Yace:

Allah Yana Cikin Taimakon Bãwa, Matuqar Bãwa Yana Taimakon Dan Uwansa

.

NA UKU (3)-

* ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ

ﻭﻷﻥ ﺃﻣﺸﻲ ﻣﻊ ﺃﺧﻲ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺣﺎﺟﺘﻪ ، ﺃﺣﺐّ ﺇﻟﻲَّ ﻣﻦ ﺃﻥ ﺃﻋﺘﻜﻒ ﻓﻲ ﺍﻟﻤﺴﺠﺪ ﺷﻬﺮﺍً،

( ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ )

Manzon Allah (saw) Yace:

Wallahi In Kasance Cikin Biyan Buqatar Dan Uwana Musulmi, Yafi Soyuwa Agareni Akan  Inyi E'itikhãfi Na Wata Daya A Masallaci

.

NA HUDU (4)-

* ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ

ﻭﻣﻦ ﻣﺸﻰ ﻣﻊ ﺃﺧﻴﻪ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻓﻲ ﺣﺎﺟﺘﻪ ﺣﺘﻰ ﻳﺜﺒﺘﻬﺎ ﻟﻪ، ﺛﺒﺖ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻗﺪﻣﻪ ﻳﻮﻡ ﺗﺰﻝ ﺍﻷﻗﺪﺍﻡ،

( ﺍﻟﺴﻠﺴﻠﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ)

Manzon Allah (saw) Yace:

Duk Wanda Ya Tafi Tare da Dan Uwansa Musulmi Cikin Biyan Buqatar Sa, Har ya Tabbatar Masa Da Buqatar Sa, Allah Zai Tabbatar da Diddigen Sa Ranar da Digadigai Zasu Zame (Akan Siradi)

.

NA BIYAR (5)-

ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ

ﺃﻓﻀﻞ ﺍﻷﻋﻤﺎﻝ ﺃﻥ ﺗﺪﺧﻞ ﻋﻠﻰ ﺃﺧﻴﻚ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ ﺳﺮﻭﺭﺍً، ﺃﻭ ﺗﻘﻀﻲ ﻋﻨﻪ ﺩﻳﻨﺎً، ﺃﻭ ﺗﻄﻌﻤﻪ ﺧﺒﺰﺍً،

( ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ)

Manzon Allah (saw) Yace:

Mafificin Aiki Acikin Ayyuka Shine: Ka Sanya Farin Ciki ga Dan Uwanka Mumini, Ko Ka Biya Masa Bashin da Ake Binsa, Ko Ka Ciyar dashi Abinci

.

NA SHIDA (6)-

ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ

ﻣﻦ ﻳﺴﺮ ﻋﻠﻰ ﻣُﻌﺴﺮ , ﻳﺴﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻭﺍﻵﺧﺮﺓ،

( ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ)

Manzon Allah (saw) Yace:

Duk Wanda Ya Sauqaqa Ma Wanda Yake Cikin Qunci, Allah Zai Sauqaqa Masa Acikin Duniya da Lahira 

.

NA BKWAI (7)-

ﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ

ﻣﻦ ﺳﺮﻩ ﺃﻥ ﻳﻨﺠﻴﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﻛﺮﺏ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﻓﻠﻴﻨﻔﺲ ﻋﻦ ﻣﻌﺴﺮ،

( ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ)

Manzon Allah (saw) Yace:

Duk Wanda Yake Son Allah Ya Tseratar dashi daga Quncin Ranar Alqiyamah, To ya Yaye Damuwar Wanda Yake Cikin Tsanani.

.

NA TAKWAS (8)-

IBNUL QAYYIM (RH) YACE:

إن في قضاء حوائج الناس

لذة لا يعرفها ‏إلا من جربها 

Lallai Acikin Biyan Buqatun Mutane Akwai Wani Dandano,  da Babu Wanda Yasanshi Sai Wanda Ya Jarraba

فافعل الخير مهما استصغرته

فإنك لا تدري أي حسنة تدخلك الجنه

Ka Aikata Alkari ga Mutane Duk Yadda Kake Ganin Qanqantar Sa,

Domin Baka San Wani Aikine Zai Shigar Dakai Aljannah ba.

.

NA TARA (9)-

قال رسول الله صلى الله عليه وسلام

خير الناس من ينفع الناس [متفق عليه]

Manzon Allah (saw) Yace:

Mafi Alkairi Daga Cikin Mutane, Shine Wanda Mutane Ke Amfanuwa Dashi.

.

Yaa Allah Kasa Mu Zamto Alkairi ga Mutane, Ba Sharri A Garesu ba.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post