INA MAZA MASU NEMAN YAWAN RUWAN MANIYI ?


Yau insha Allah zamuy magana akan hanyar da namiji zaibi domin kara samun ruwan maniyyi. 

Duk namijin dake son ya samu yawan ruwan maniyi mai kauri kuma mai inganci to sai ya nemi dabino guda goma ya cire kwallan ya jefar sai yadaka dabinon ya zuba ruwa masu dumi ya gauraya sai a washe gari ya nemo peak ta gongoni, guda daya sai yazuba a cikin cup na tea ya hade da ruwan dabinon a guri daya ya gauraye su sai ya raba kashi biyu ya sha, kashi daya da safe kashi daya da yamma, 

Yawan ruwan maniyi a jikin namiji, shi ke nuni da karfin sha'awar dake gare shi. Ita kuma sha'awa ita kan sa namiji yaji yana da bukatar saduwa da iyalin shi. kuma a lokacin saduwa matar zata ji shi da karfin da ya kamata, wanda hakan kansa ma'aurata nishadi da matukar jin dadi da kuma zubarda maniyi mai tarin yawan gaske da biyan bukata a lokacin inzali.

Yawan maniyin dake fita a yayin inzali yakan sa namiji samun gamsuwa tamkar bai taba saduwa da mace ba. 

A yayinda karamcin ruwan maniyi Kansa  namiji yayi inzali ba tare da jin wani dadi kamar yanda ya kamata ba. Wannan kan rage kwazo da karfin namiji a yayin saduwa.

Lokuta da dama namiji kan ji shawarsa na ja baya, sai ya rinka tunanin ai watakila basir ne musamman a al'adar malam Bahaushe, alhali da akwai abubuwan da basu da alaka da basir masu haifarda haka.

Namijin dake bukatar samun yawan maniyi to zai dakata daga yawan jima'i, sai ya nemi kwan kaza guda biyu da albasa da man zaitun sai ya soya kada a saka maggi amma a saka gishiri kadan.

A tabbatar an soya da kyau, sai a ci da safe ko yamma. wasu albasa na kumbura masu da ciki, amma idan aka soya ta soyu to ba wani lahani da zata haifar.

Kada a rinka ci har a koshi, domin ba tuwo bane, da ake yiwa cin mai jin yunwa, shi kwai protein ne ba carbohydrate bane dan haka kadan ake ci bawai a cika plate za ayi a zauna ayi ta faman ci ba, za a ci daidai azanci.

Haka kuma za a iya cin kwan zabuwa dafaffe, ba wanda aka soya ba, idan an ci da safe to sai a nemi kunun alkama da yamma sai a sha.

A ringa yin haka akai-akai, za a yiwa Allah godiya.

Alhamdulillah.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post