ABINCIN DAKE KARAWA NAMIJI RUWAN MANIYYI DA SHA'AWA


Shin ko kunsan irin nau'in abincin da ya kamata ma'aurata su ringa ci domin karin sha'awa da karin ruwan maniyyi, karanta wannan rubutu har karshe.

Ya kamata mutane su san cewa yawan ruwan maniyi ga jiki shi ke sa jin sha'awa da kuma samun damar maimaita jima'i a lokaci guda. A duk sanda namiji ya yawaita yin jima'i ba tareda samun abinci mai gina jiki da maye gurbin abinda ke fita a jikinsa ba, to a hakika zai raggwanta domin karfin jikinsa ne ke tafiya, saboda shi maniyi yana dauke da sinadiran carbohydrate da calcium (wanda sune ke samarda karfi ga jiki da kuma qassa) kaga kenan a duk sanda maniyi ke fita to karfin jikine ke fita, wannan ne yasa a lokuta da dama bayan an kammala jima'i namiji yakan jin jikinsa yayi liqis, ba karfi duk jiki yabi ya mutu, sabanin mace wanda ita ba wani abu dake fita a jikinta ballantana ace tana raguwa. 

A hakika yawan jima'i ba abinci mai kyau to illa ce babba, dan takan lalata karfi da kuzarin namiji kana tafiya iska na daukarka, duk kabi ka rame ka koma wani iri ba wani kuzari a tare da kai sai gashin fuska da kwantsa a ido. kuma zaka rasa karfin biyawa matarka da bukata, ga mata da jarraba musamman a lokacin zafi.

Abincin da ya dace magidanci ya ring a amfani dasu domin samun lafiya da kuzari su ne;

(1) Alkama

A nemi alkama a rinka yin kununta ana sha akai-akai, kada a zuba sugar, za'a iya tauna garinta idan ana bukata. Hakika tana samarda yawan ruwan maniyi da karfin jima'i.

(2) Dabino

A nemi dabino mai kyau a cire qwallan sai a jika a cikin ruwan dumi, washe gari a nemi madara mai kyau sai a hada da ruwan dabinon misalin cup daya a zuba a shanye, a rinka yin haka akai-akai, za'ayi mamaki.

(3) Kwan kaza

Ana iya neman kwan kaza na hausa kamar guda uku da albasa mai kyau sai a fasa kwan a soya a sanya albasa kada a bari yaqone ayi shi jagab-jagab haka sai a ci, a nemi tea mai kauri wanda yasha rabin gongonin peak milk amma kada a saka suga da yawa sai a sha.A kula da yin haka.

(4) kayan Marmari

A rinka shan kankana da abarba da lemuo akai akai. Haka kuma za'a iya neman ruwan albasa rabin cup da ruwan zuma rabin cup a tafasa sai a rinka sha za'a sha mamaki da iznin Allah.

Alhamdulillahi! 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post