YADDA BUDURCIN 'YA MACE YAKE

 


Budirci yanada muhimmanci awajen kowacce mace shiyasa duk wacce ta rasashi jikinta yake sanyi tun kafin ta shiga gidan miji kasancewar duk yanda take burge mijinta matukar ya fahimci ta rasa budircinta dole zaiyi zargin wani abu kuma wannan shima yana daya daga cikin masomin tashin hankali kamar yadda yake faruwa awannan zamanin. 

To amma acewar wani shaharraren likitan mata Dr Joseph mwaka cewa yake memakon ayita wayarwa da mata kansu akan budurci zaifi kyau amaida hankali a wajen wayarwa maza Kansu a kan abinda yashafi budurci ta yanda namiji koda yaji mace akasin yanda yake tsammani bazaiyi zargintaba domin kawai yanzu abinda samari suka yarda dashi farkon saduwa da mace suga jini shine yake tunanin cewa ya auri budurwa yana ganin sabanin haka zai fara zarginta to kunga daga Wannan lokacin soyayyar da yakeyi mata ansamu gibin 70% to yaya kuke ganin rayuwar auren zata kasance.

A takaice muma zamuyi amfani da Shawarar Dr Joseph na wayarwa maza Kansu akan abinda ya shafi budurcin mace saboda wasu matan sunyi iya kokarinsu wajen kiyaye kansu Amma daga karshe miji yarinka zarginsu wadansu Kuma kaddarace ta fado kansu babu yanda suka iya ita Kuma kaddara bata bada zabi

Koda yake saninmu bekai nanba amma yanda naga wasu matan sun samu Kansu awannan yanayin shine naga ya kamata nafadi abinda nasani sauran bayani Kuma aci gaba da bincike Wannan kalubale ne babba a wajen ma aurata matukar ango ya fahimci budircin amarya ba daidai ba

INA BUDIRCIN MACE YAKE?

Masana sunyi bayani kala hudu Kuma kowanne bangare da dalilansu ga bayani da dalikan da suka bayar Kamar haka;

(1) kashi na farko sunce fatarda take tsakiyar farjin mace wacce ta toshe kofar farjin itace take fashewa kuma tana fashewane ta hanyoyi da yawa musamman kamar saduwa da namiji ko bude kafa ko hawa wani abu ko gudu, da dai sauransu amma kuma dolene idan ta fashe aga jini suna cewa matukar ango bega jiniba daren farko to wannan budircinta ya fashe abaya. 

(2) wasu kuma sukace budurcin mace wani ruwane me kamada na ni'ima kuma kowacce mace tana dashi yana zuwane a lokacin da ta fara saduwa da namiji kuma namiji zaiji wani irin dadi saboda duk jikin mace wannan ruwan yafi komai dadi amma ita kuma zafi takeji a lokacin da yake fita kuma ruwan farine amma akwai alamar jini ajikinsa to wannan shine ruwan budurci kuma kowacce mace sau daya yake fita to ta wannan hanyar ake ganewa mace ta taba saduwa da wani koda tana bude Wannan ruwan zaizo

(3) wadannan kuma sukace budurcin mace yar wata karamar tsokace a saman farji Wanda kuma don an saka yatsa ko azzakarin namiji baya fashewa saidai idan haihuwa tayi. Abinda suke nufi anan duk abinda shiga yayi ba fitaba baya fasashi duk dadewar mace tana saduwa da namiji matukar bata haihu ba to yana nan amma daga ta haihu zai fashe kofar ta bude dole sai anyi yan dabaru zai koma suna ganin don mace ta sadu da namiji kwanaki kadan wajen zai hade. 

(4) na hudu kuma cewa sukayi sun yarda budurcin mace 'yar fatace a tsakiyar farji amma saduwa da ita baya fasa matashi saboda shi kansa saduwa da mace kala ukune

  • Akwai Wanda za a sadu da ita tana budurwa ta balaga kuma tanaso to wannan budurcinta baya fashewa saboda sha'awarta ta motsa kuma idan mace Sha'awarta ta motsa ruwa yana taruwa a farjinta kuma yana budewa sannan fatar budurcin tana dagawa
  • Akwai kuma wanda za ayi bataso ma'ana da karfi za'ayi mata to wannan shi zai iya fasa budurcin saboda Sha'awarta bata motsa ba
  • Sai kuma wacce za'a yiwa mace tana karama wacce bata balaga ba shima budurcin yana fashewa Koda kuwa tanaso akayi ko bata so.
Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post