ZoyaPatel
Ahmedabad

Abubuwa 5 da Ke Janyo Fashewar Faifan Ƙashin Baya: Alamomi, Dalilai da Hanyoyin Kariya

Abubuwa 5 da Ke Janyo Fashewar Faifan Ƙashin Baya: Alamomi, Dalilai da Hanyoyin Kariya
Abubuwa 5 da Ke Janyo Fashewar Faifan Ƙashin Baya


Ciwon baya na daga cikin matsalolin lafiya da mutane da dama ke fama da su, musamman manya da masu yin ayyukan da ke buƙatar amfani da jiki sosai. Daya daga cikin manyan dalilan da ke haddasa matsanancin ciwon baya shi ne fashewa ko bullin faifan ƙashin baya, wanda a turance ake kira Herniated Disc ko Slipped Disc.

Wannan matsala na iya haddasa ciwon baya mai tsanani, zafin ƙafa, dindiris, rauni a ƙafafu, da wahalar tafiya idan ba a kula da ita da wuri ba.

A wannan maƙala, za mu yi bayani kan menene faifan ƙashin baya, alamomin matsalarsa, abubuwa biyar da ke janyo fashewarsa, da hanyoyin kariya.

Menene Faifan Ƙashin Baya?

Ƙashin gadon baya (Spine) wata muhimmiyar jigi ce a jikin ɗan Adam, wacce ta ƙunshi jerin ƙasusuwa har kusan 33, daga ƙasan kai har zuwa ƙugu.

A tsakanin kowanne ƙashi akwai wani abu mai laushi kamar roba ko ɗanko wanda ake kira:

Faifan ƙashin baya (Disc)

Aikin wannan faifai shi ne:

1. rage gogayya tsakanin ƙasusuwa
taimaka wa baya ya lanƙwashe ya miƙe cikin sauƙi
2. ɗaukar nauyin jiki da rage matsin lamba
3. kare jijiyoyin laka (spinal nerves)

Lokacin da wannan faifai ya fashe ko ya yi bulli, yana iya danne jijiyoyin baya, wanda hakan ke haifar da ciwo da wasu matsaloli.

Alamomin Fashewar Faifan Ƙashin Baya

Idan faifan baya ya samu matsala, mutum na iya fara fuskantar wasu daga cikin waɗannan alamomi:

1. Matsanancin Ciwon Baya

Ciwon na iya farawa daga ƙasan baya, musamman a yankin ƙugu.

2. Ciwon da Ke Sauka Zuwa Ƙafa

Mutum na iya jin ciwo yana sauka zuwa:

  • ɗuwawu
  • cinya
  • sangalali
  • har zuwa tafin sawu

Wannan yawanci alamar jijiya ta danne ne.

3. Jin Zogi ko Dindiris

Wasu kan riƙa jin:

  • kamar ana tsitstsira allura
  • kamar ana tafiyar da wutar lantarki
  • zafi mai tsanani
  • kaikayi ko kamar tafiyar ƙwari a ƙafa

4. Rauni a Ƙafafu

Ƙafafu na iya rasa ƙarfi, tafiya ta yi wahala, ko mutum ya kasa yin ayyukan yau da kullum yadda ya saba.

Abubuwa 5 da Ke Janyo Fashewar Faifan Ƙashin Baya

Ga manyan abubuwan da ke ƙara haɗarin samun wannan matsala:

1. Ƙiba ko Yawan Nauyin Jiki

Yawan kiba na ƙara wa ƙashin baya nauyi fiye da yadda ya kamata.

Wannan nauyi yana matsa wa fayafayan baya lamba, wanda ka iya janyo:

  • bulli
  • tsagewa
  • fashewa

Rage kiba na daga cikin hanyoyin kare baya.

2. Ayyukan Da Ke Buƙatar Nauyi

Mutanen da ke yawan:

  • ɗaga kaya masu nauyi
  • jan kaya
  • turawa
  • aikin gini
  • aikin gona mai wahala

na cikin masu haɗarin samun matsalar faifan baya.

Haka nan, motsa jiki ba tare da kulawa ba, musamman ɗaga nauyi a gym, na iya jawo matsalar idan ba a yi shi yadda ya dace ba.

3. Shan Taba Sigari

Masana sun nuna cewa shan taba na rage iskar oxygen da jini da ke kai wa fayafayan baya.

Hakan na rage lafiyarsu, ya sa su tsufa da wuri, kuma su fi saurin lalacewa.

4. Tuƙi Akai-Akai

Mutanen da ke yin dogon tuƙi kullum — kamar:

  • direbobi
  • masu mota a doguwar tafiya
  • masu aiki da manyan motoci

na iya samun matsalar baya saboda:

1. jijjiga jiki
2. zama na tsawon lokaci
3. matsin lamba a ƙasan baya

5. Rashin Motsa Jiki

Zama wuri guda ba tare da motsa jiki ba na sa tsokokin baya su yi rauni.

Lokacin da tsokoki suka yi rauni, ƙashin baya da fayafayansa sukan ɗauki duk nauyi, wanda ke ƙara haɗarin matsala.

Yadda Ake Kare Kai Daga Matsalar Faifan Baya

Domin rage haɗari:

✔ ka rage kiba idan kana da nauyi fiye da kima
✔ ka guji ɗaga kaya ba daidai ba
✔ ka daina shan taba
✔ ka riƙa motsa jiki akai-akai
✔ ka guji zama ko tuƙi na tsawon lokaci ba tare da hutu ba
✔ ka nemi shawarar likita idan kana fama da ciwon baya mai tsanani

Muhimmancin Ganin Likitan Fisiyo

Likitan fisiyo (Physiotherapist) na taimakawa wajen:

  • rage ciwo
  • gyara matsalar daga tushe
  • koyar da atisayen da suka dace
  • rage yiwuwar tiyata

Yawan shan magungunan rage zafi ba tare da duba ƙwararren likita ba, na iya ɓoye matsalar na ɗan lokaci amma ta ƙara muni daga baya.

Kammalawa

Fashewar faifan ƙashin baya matsala ce mai tsanani wacce ka iya shafar rayuwar mutum gaba ɗaya idan ba a kula da ita ba.

Abubuwa kamar:

  • ƙiba
  • ɗaga kaya masu nauyi
  • shan taba
  • tuƙi akai-akai
  • rashin motsa jiki

duk suna ƙara haɗarin kamuwa da ita.

Idan kana yawan jin ciwon baya ko ciwon ƙafa da ke sauka ƙasa, yana da kyau ka nemi shawarar ƙwararren likita da wuri.


[Related Posts]
Mumbai
Kolkata
Bangalore
Previous Post Next Post