ZoyaPatel
Ahmedabad

YADDA AKE BINCIKEN NEMAN AURE – BAYANI NA ILIMI DA AIKI

YADDA AKE BINCIKEN NEMAN AURE – BAYANI NA ILIMI DA AIKI

YADDA AKE BINCIKEN NEMAN AURE – BAYANI NA ILIMI DA AIKI


Tambayar “ya ake binciken neman aure?” tambaya ce mai matuƙar muhimmanci, musamman a wannan zamani da boyayyun halaye suka yawaita, kuma mutane da yawa suna iya nuna fuska daban kafin aure, su sauya bayan aure.

Abin fahimta na farko shi ne:

Ba duk wani hali ake iya ganowa da bincike ba, amma hakan ba hujja ba ce ta yin sakaci.
Abin da ake iya ganowa, wajibi ne a nemo shi.

Yawanci abin da ke lalata bincike su ne:

  • gaggawa da zumudin aure
  • kallo da ido kawai (beauty, kudi, takardu)
  • tsoron “kar a tsangwama mai nema”
  • rashin tura mutanen da suka dace suyi bincike

A Musulunci, binciken aure amanace, kuma duk wanda aka tambaya ya san gaskiya ya boye, yana cikin zunubi.

MUHIMMIN TSARI: BINCIKE GIDA UKU (3)

1️⃣ Bincike KAFIN A FARA NEMA

Wannan shi ne ginshikin nasara. Idan aka yi kuskure anan, komai na gaba yana da rauni.

1.1 Mahaifa / Asali

Asalin mutum yana da matuƙar tasiri:

  • irin tarbiyyar da ya tashi a ciki
  • halayen iyayensa
  • yadda iyali ke mu’amala da jama’a

Ana tambaya:

  • dattijai
  • makwabta na baya
  • matasa da mata (saboda bayanai sun fi yawo a cikinsu)

A nan ba a tambayar mutum daya kacal ba, ana hada bayanai daga bangarori daban-daban.

1.2 Unguwa / Mazauni

Unguwa ita ce madubi:

  • idan namiji: alaƙarsa da masallaci
  • halayensa da makwabta
  • abokan zama da na yawo

Idan mutum yana yawan sauya wuri:

A tambayi dalilin barin wuraren baya, domin gudu daga matsala ma alama ce.

1.3 Wajen Aiki / Sana’a

Wurin aiki yana bayyana:

  • gaskiya ko rikon amana
  • ladabi da hakuri
  • yadda ake mu’amala da mutane

A kula: akwai makiya. Saboda haka:

  • a tambayi mutane fiye da daya
  • a gwada bayanai kafin yanke hukunci

1.4 Makaranta

Makaranta tana bada:

  • tarihin halayya
  • tarbiyya
  • daukar nauyi

Tambaya na iya zuwa:

  • shugaban makaranta
  • malamai
  • abokan karatu

Idan aka ce mutum baya zuwa makaranta ko yana da matsala, a binciki dalili, ba a yanke hukunci kai tsaye ba.

1.5 Iyaye da Gidan Mai Nema

Wannan ana yawan mantawa da shi, alhali yana da muhimmanci sosai.

Domin:

  • aure ba mutum daya ake aura ba
  • iyaye da iyali suna da tasiri kai tsaye

A duba:

  • rikice-rikicen gida
  • tsoma bakin iyaye
  • dabi’un mu’amala

Idan wannan mataki na farko ya gamsar → sai a bada damar ci gaba da nema.

2️⃣ BINCIKE BAYAN AN FARA NEMA

Bincike baya tsaya wa. Mutum na iya sauya hali cikin kankanin lokaci.

2.1 Zama Tsakanin Mai Nema da Iyaye

Wannan ba hira kawai ba ce, gwaji ne:

  • cin abinci tare
  • lura da ladabi
  • lura da sallah
  • yadda yake amsa tambayoyi

Ana iya:

  • yin tambayoyi kai tsaye
  • rubuta bukatu da sharudda
  • neman ganin dukiya da ido, ba da baki ba

2.2 Tattaunawar Masu Nema da Juna

Wannan shi ne zuciyar binciken:

  • fahimtar addini
  • ra’ayi kan aure
  • hakkoki da nauyi
  • abokai da dabi’u
  • tarihin rayuwa

Tambaya kai tsaye ba laifi ba ne idan an yi cikin ladabi.
Rubuta tambayoyi yana taimakawa hana mantuwa.
A kula da sabani a zance (inconsistency).

2.3 Haduwa da ‘Yan Gida

Ta wannan hanya:

  • ana ganin tarbiyyar gida
  • yanayin mu’amala
  • gaskiyar labaran da aka fada

Ko da ta waya ne, yana da amfani sosai.

2.4 Haduwa da Abokai / Kawayen Juna

Aboki madubin mutum ne.

  • kalar abokansa
  • irin hirarsu
  • dabi’unsu

Daga nan ana samun hint mai yawa.

Wannan bincike yana ci gaba har zuwa ranar aure.
Aure da yawa an fasa su:

  • saura kwana
  • ko ma ranar daurin aure

Wannan ba asara ba ce, tsira ce.

3️⃣ WA YA DACE YA YI BINCIKE?

Ba kowa bane ya dace:

  • dole ya zama mai addini
  • mai hankali da gogewa
  • wanda yake sanin mutane
  • wanda ba zai gajiya ba

Uba na iya:

  • zuwa da kansa
  • wakilta amintacce
  • ko daukar kwararre (lauya, journalist, investigator)

KAMMALAWA TA ILIMI

Idan aka yi bincike da gaske:

  • mutum ya sauke hakkin sa a wajen Allah
  • ko matsala ta taso, Allah yana kawo mafita
  • ana rage nadama bayan aure

Rashin bincike:

  • shi ne tushen yawancin matsalolin aure
  • shi ke sa a rika cewa “da mun sani”

Allah ya ba mu aure na alkhairi, ya kare mu daga boyayyun halaye, ya sa mu yi abin da ya dace kafin mu ɗaura aure.
Wallahu a’alam.


[Related Posts]
Mumbai
Kolkata
Bangalore
Previous Post Next Post