![]() |
| ABUBUWAN DA YA KAMATA KI SANI KAFIN A MIKI AURE |
’Yan mata da dama suna shiga aure ba tare da sun samu cikakken shiri ba, ko kuma ba a sanar da su muhimman abubuwan da za su taimaka musu wajen inganta zaman aure. Wannan rashin shiri yana sa wasu maza su shiga damuwa, wasu su kasa hakuri, har ma wasu su nemi wata matar ko su bar auren gaba ɗaya.
Don haka, ga wasu muhimman abubuwa da duk wata mace ya kamata ta sani, ta kuma kware a kansu kafin aure:
1️⃣ Tsabta
Dole ne mace ta koyi tsaftar jiki da muhalli.
Wasu mata, musamman daga gidajen da ake musu hidima sosai, suna girma ba tare da sun saba tsaftace kansu ko muhallinsu ba. Wannan ba daidai ba ne.
Idan mace ta iya kula da muhallinta, to tabbas za ta iya kula da jikinta.
Tsabta tana kara daraja da kwanciyar hankali a gidan aure.
2️⃣ Ilimi
Ilmi yana daga cikin ginshikan rayuwar mace kafin aure.
- Ilmin addini wajibi ne iyaye su koya wa ’ya’yansu mata kafin aure.
- Ilmin zamani kuma yana taimakawa mace wajen fahimtar mijinta, tarbiyyar ’ya’ya, da mu’amala da al’umma.
Mace marar ilimi tana fuskantar wahala wajen mu’amala da miji da kuma tarbiyyar ’ya’yanta.
3️⃣ Sana’a ko Abin Yi
Lokacin dogaro kacokan da miji ko iyaye ya wuce.
Yana da matuƙar muhimmanci mace ta:
- mallaki sana’a
- ko ilmin da zai ba ta damar samun kudin shiga
Dogaro da miji kan duk wani abu, har da wanda ba wajibi ba, yana haddasa sabani a aure.
Kuma namijin da bai yarda matarsa ta yi aiki ko sana’a ba, alhali halal ne, ya kamata a yi tunani sosai a kansa.
4️⃣ Hakuri
Hakuri ginshiƙi ne na zaman aure.
Duk macen da ba ta iya hakuri ba, za ta wahala a aure.
A wasu lokuta, ko da kina da gaskiya, hakuri da yafiya suna kare zaman lafiya.
5️⃣ Iya Mu’amala da Mutane
A gidan aure ba ke kadai ba ce.
Akwai:
- ’yan uwan miji
- abokansa
- makota
- masu hidima (idan akwai)
Yadda za ki tarbi mutane shi ne zai sa su sake zuwa ko su guje ki.
Koyon mu’amala tun kafin aure yana da matuƙar muhimmanci.
6️⃣ Girki
Duk wanda ya ce girki ba aikin mace ba ne a gidan aure, yaudararki yake yi.
Matan Manzon Allah (SAW) suna masa girki, har ma baki sukan ci.
Iya girki na kara shiga zuciyar miji, kuma yana taimakawa zaman aure sosai.
Mace mai iya girki:
- tana sa mijinta jin daɗin zama a gida
- tana rage masa sha’awar cin abinci a waje
7️⃣ Kyauta
Mace kada ta zama:
- marowaciya
- mai ƙwaro
- ko mai tsuke hannu fiye da kima
Kyauta tana gina soyayya tsakanin:
- miji da mata
- mata da baki
- uwa da ’ya’ya
Ba a nufin ki yi abin da ya fi ƙarfinki ba, amma ki bayar da abin da kika iya cikin hikima.
8️⃣ Iya Adanawa
Adana dukiya da sirri alama ce ta balaga.
- Duk wani abu na mijinki da kika gani, ki adana masa.
- Abinci da kaya da aka bar a hannunki, ki kula da su da kyau.
- Sirrin gida ya zama sirrinki.
Wannan dabi’a ana koya ta ne tun daga gida, kafin aure.
9️⃣ Iya Magana
Magana da miji ba iri ɗaya ba ce da magana da iyaye ko kawayenki.
Akwai kalmomin da:
- ba a furtawa miji ko da kuna wasa
- ba a faɗa masa ko da yana cikin fushi
Koyon yadda ake magana da miji hikima ce mai matuƙar muhimmanci a aure.
🔟 Ilimin Jima’i
Wannan muhimmin bangare ne da ake yawan jin kunyar koyar da ’ya’ya mata.
Rashin sanin abubuwan da suka shafi jima’i kafin aure:
- na iya jawo matsala a rayuwar aure
- musamman idan mijin ya taba aure ko yana da kwarewa
Yana da kyau iyaye mata:
- su cire kunya
- su ilmantar da ’ya’yansu mata
- ko su nemi dattijai nagari masu ilimi su yi hakan
KAMMALAWA
Idan mace ta shiga aure da:
- ilimi
- tarbiyya
- hakuri
- kwarewa
za ta samu zaman aure mai inganci da albarka, da yardar Allah.
Allah Ya amfanar da ’yan mata, Ya kyautata aurensu, Ya ba su zaman lafiya
